Yara 70,000 na cikin barazanar mutuwa a Najeriya

Yara 70,000 na cikin barazanar mutuwa a Najeriya

- Talauci zai kasance babban kalubale a sansanin yan gudun hijira daban-daban a arewa maso gabas nan bada jimawa ba

- Wani kungiyar taimako, na ceton yara, na rokon kasashen waje da su zo su taimaki yara a sansanin

Yara 70,000 na cikin barazanar mutuwa a Najeriya
Yara na cikin hatsari a sansanin yan gudun hijira har sai kasashen waje sun taimaka

Kasar Najeriya na cikin hatsarin rasa kimanin yara 70,000 a shekara ta 2017, kungiyar agaji, na ceton yara, ta bayyana a yayinda take rokon kasashen waje da suyi gaggawan taimako gurin yaki da yunwa, tamowa da cututtuka a kasar.

Aikin ta’addanci yafi illata yara da kuma wadanda ke sansanin yan gudun hijira a fadin arewa maso gabashin Najeriya, a cewar wata rahoto daga jaridar Daily Trust.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa hudu game da gwamnatin Buhari

Rahoton ya nuna kalamin shugaban kungiyar na taimakon yara a Amurka, Kevin Watkins, cewa yayi roko na musamman kan cewa kasashen waje su shigo lamarin don su tallafi gwamnatin Najeriya da kayayyaki domin ceto rayukan jama’a da yawa.

Watkins, ya ziyarci aikin kungiyarsa a arewa maso gabas, yace yawancin asibitocin dake maganin ciwon yunwa a cike yake da marasa lafiya.

Yace ko wani asibiti na fama da matsalolin marasa lafiya dake fama da ciwon yunwa mai tsanani, ya kara da cewa: “Muna cikin wani hatsari mai girma na ganin sama da yara 70,000 zasu rasa rayukansu cikin sabon shekara.

 “Za’a iya magance abun. Amma idan muka ci gaba da harkoki kamar yadda muka saba a yanzu, hakan zai faru.

KU KARANTA KUMA: Tinubu ya bar Najeriya ba saboda Oyegun ba

 “Idan yara suna wahala, wajibinmu ne muhada kai mu kawo canji. Kowa na da fasaha, da kuma kwarewa. Lokaci yayi da zamu aiki gaba daya.”

Ya ci gaba da cewa: “Kasashen waje su goya ma kasar Najeriya baya don taimakawa gurin magance wannan halin kunci da jama’a ke ciki."

Asali: Legit.ng

Online view pixel