Bani na kashe Kudirat Abiola ba – Al-Mustafa

Bani na kashe Kudirat Abiola ba – Al-Mustafa

- Major Hamza Al-Mustapha ya jadda cewa aikinshi lokacin Abacha shine bayar da tsaro

- Ya musanta kisan Abiola kamar yadda ake yadawa

Bani na kashe Kudirat Abiola ba – Al-Mustafa
Kudirat Abiola

Major Hamza Al-Mustapha yayi Magana akan mutuwar Kudirat Abiola kuma ya musanta hannunshi aikin abubuwan da suka tattari mutuwarta.

Major Hamza Al-Mustapha ya kasance mai tsaron marigayi Janar Sani Abacha kuma ana jingina shi da kisan uwargidan Abiola, wanda ya lashe zaben shekarar 1993 amma Babangida ya danne.

KU KARANTA: Yadda na sa ‘ya ‘yana 14 fashi da makami –Tsohon barawo

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa Major Hamza Al-Mustapha yayi Magana ne a lakcan Dr. Fredrick Fasehun a Akure a ranan Laraba,9 ga watan Nuwamba inda ya wanke kansa daga kisan ta.

Yace: “Ana bata mini suna, nayi aikina ne yadda ya kamata na tsare shugaban kasa, kare gwamnati da mutanen kasa.

Yayi kira dan yan Najeriya su hada kai domin kawo cigaban Najeriya duk da bambance-banbancen siyasa.

Yace: “Akwai taratsi da yawa, rowa, da son kai. Muna ci baya ne kullun. Damuwa na shine a so kasan nan kuma a taimakawa cigaban ma’aikatu ba lalata sub a. abinda ya kamata mu lura da shi kenan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel