Kamfanin shell ya rufe ma'aikatantar sa a yankin Neja Delta

Kamfanin shell ya rufe ma'aikatantar sa a yankin Neja Delta

- A Najeriya, kamfanin mai na Shell, ya ce ya rufe tashar samar da iskar gas ta Escravos da ke yankin Neja Delta mai azrikin man fetur.

- Sanarwar na zuwa ne sakamakon zanga-zangar da wasu mazauna yankin suka yi a ranar Laraba.

Kamfanin shell ya rufe ma'aikatantar sa a yankin Neja Delta
shell pipeline

A cikin wani sakon email da ya aikewa manema labarai, kamfanin na Shell din ya ce zai cigaba da ayyukansa a Escravos din idan masu zanga-zangar sun watse.

KU KARANTA KUMA: Sanatoci na shirin watsi da bukatar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Masu zanga zangar sun kwashe kwanaki takwas suna gudanarwa, inda suka yi korafin rashin ababem more rayuwa a yankin.

Mai karatu zai iya tunawa cewa ajiya ma dai Tsagerun nan na Neja Delta da kewa kansu lakabi da Niger Delta Avengers (NDA) sun dauki alhakin kai harin da yayi sanadiyyar fasa wani bututun mai na Trsan Forcados  dake a cikin dazukan karamar hukumar Warri ta kudu a jihar Delta.

Mai magana da yawun tsagerun na Niger Delta Avengers (NDA) Mudoch Agbinibo ne ya sanar da haka a cikin wani jerin sako da ya wallafa a shafin sa na Tuwita mai adreshi @agbiniboND a jiya Laraba inda yace wannan yana zaman kashedi ne ga sauran kamfunnan man kasar nan dake a yankin na Neja Delta inda kuma ya jadda aniyar su ta ci gaba da kai irin wadannan hare-haren a dukkan bututun man dake a yankin nasu.

Wannan sabbin hare-haren dai suna zuwa ne kimanin awanni 24 bayan wani bututun man da wasu tsagerun da ba'asan ko suwaye ba suka fasa a wani wurin daban duk dai a cikin jihar ta Delta a sanyin safiyar jiya.

Kafin dai daukar alhakin kai harin da Niger Delta Avengers (NDA) tayi, a safiyar yau kamfanin jaridar Daily Post ta wallafa rahoton cewa bututun man da aka fasa na Trans Forcados yana fidda mai ne daga kauyen Batan na jihar ta Delta.

https://youtu.be/4Hx0Xu2KLSk

Asali: Legit.ng

Online view pixel