Tirkashi! Auren wada da doguwa

Tirkashi! Auren wada da doguwa

Anyi auren ban mamaki a kasar Wales na masarautar Birtanya inda wani wada mai suna James Lusted mai shekaru 28 ya auri budurwarsa Chloe.

Tirkashi! Auren wada da doguwa

Sai dai saboda tsananin gajartan James, sai da aka daura shi saman wani kwaranga sannan ya iya sumbatar amaryar tasa a ranar bikin aurensu, James yace amfanin kwarangar shine don ya dinga kallon amaryarsa ido-da-ido a yayin gabatar da sigar daurin auren.

Tirkashi! Auren wada da doguwa

James ya cigaba da fadin musamman ya sanya aka hada masa wannan kwarangar, kuma ma idan yah au ta yafi amaryarsa tsawo da kadan, yace ta haka ne kadai zai samu damar sumbatar amaryar tasa yadda aya kamata.

Tirkashi! Auren wada da doguwa

KU KARANTA: An watsa ma kyakkyawar budurwa ruwan guba

Tirkashi! Auren wada da doguwa

Ita kuwa amarya Chloe tace tana matukar kaunar angonta duk da wadantar sa, tace gajartansa bai dame ta indai da so da kauna.

Tirkashi! Auren wada da doguwa

An daura auren ma’auratan ne a cocin St. Margareth dake garin Bodewyddan, arewacin kasar Wales, sai dai wasu yan dangin Chloe sun nuna rashin amincewarsu da auren da fari, saboda irin halittar James.

Tirkashi! Auren wada da doguwa

Uwar Chloe na daga cikin wadanda suka nuna rashin amincewarsu da auren, tace bata son yarta ta auri wada, sai dai bayan ta samu ganawa da James, ta fahimce shi da irin halayyarsa, hakan sai ya canza mata tunani.

Tirkashi! Auren wada da doguwa

Ko me zaka ce kan wannan aure?

Asali: Legit.ng

Online view pixel