Michelle Nkamankeng, marubuciya mafi karancin shekaru

Michelle Nkamankeng, marubuciya mafi karancin shekaru

Sanannen lamari ne cewa akwai tarin yara masu hazaka da kokari a nahiyar Afirka, musamman idan ire iren yarannan suka yi wani gwaninta sai kaga ana mamakin shekarun nasu, tare da baiwar da Allah yayi musu.

Michelle Nkamankeng, marubuciya mafi karancin shekaru

A yayin da a wannan zamanin da yara kanana ke matukar sha’awar kale kallen finafinai da wasanni, sai ga shi an samu wata yarinya yar kasar Afirka ta kudumai suna Michelle Nkamankeng yar shekara 7 ta baje iya baiwar da Allah yayi mata domin karfafa ma yara sa’anninta gwiwar yin karatu, ta hanyar kasancewa marubuciya mafi kankantar shekaru a Afirka gaba daya.

Ita dai Michelle Nkamankeng ta wallafa wani littafi ne mai suna ‘Waiting waves’, littafin na nuna yadda yaro zai kara ma kansa kwarin gwiwa a rayuwa tare da samun yakini don samun nasara a rayuwa, abin mamaki shine yadda karamar yarinya ta iya wallafa littafi mai cike da fasaha irin wannan.

Michelle Nkamankeng, marubuciya mafi karancin shekaru

KU KARANTA: Tsohuwa ta ba Buhari Akuya

Wannan lambar yabo da marubuciya Nkamankeng ta samu ya sanya iyayenta alfahari da ita, da wannan ya zama wajibi akan iyaye da su baiwa yayansu goyon bayan da kwarin gwiwa wajen zabar aikin da suke muradin shiga a rayuwa.

Michelle Nkamankeng, marubuciya mafi karancin shekaru

Marubuciya Nkamankeng dalibar aji biyu ce a makarantar Sacred College. Ta fara rubutu tun tana shekara 6, inda ta rubuta littafinta na farko, a yanzu dai tana kan rubuta littafinta na hudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel