Shugabannin Amurka guda 4 da suka samu yawan kuri'u

Shugabannin Amurka guda 4 da suka samu yawan kuri'u

Idan aka yi misali da zaben yan Najeriya, da zaran mutun ya samu zabe mafi yawa a fadin kasar, toh zai kasance mai nasarar zaben. Duk da haka, wannan shine mafi bambanci tsakanin zaben kasar Amurka da na kasar Najeriya.

Shugabannin Amurka guda 4 da suka samu yawan kuri'u
Fitattun kuri'u a Amurka

Da misalign karfe 2 na rana a agogon kasar Amurka, Clinton ta samu kuri’u guda 59,626,052 a fadin kasar, Trump kuma ya samu 59,427,652 kenan ta fi shi da kuri’u 198,400 amma shi yayi nasara, saboda yayi nasara a kolejoji fiye da ita, wanda haka ne kasar Amurka ke kirga kuri’un ta.

Sau nawa hakan ya taba faruwa a baya? Bari mu duba mu gani:

1. Andrew Jackson (1824)

Shugabannin Amurka guda 4 da suka samu yawan kuri'u
Andrew Jackson da Quincy Adams

Andrew Jackson ya fadi zabe a shekara ta 1824 saboda, duk da cewan ya fi samun yawan kuri’u, tazarar sa bai kai mizanin da zai sa yayi nasara ba, kuma kundin tsarin mulkin yaba da ikon cewa majalisa ce kawai zata iya yanke shawarar zabe.

Henry Clay, daya daga cikin yan takarar yaba John Quincy Adams goyon bayan sa, wani dan takaran da Adams suka lashe kuri’ar majalisa.

Adams yayi ganawa na sirri tare da Clay, ya samu goyon bayan Clay sannan kuma yayi nasarar lashe zabe. Bayan haka, ya nada Henry Clay a matsayin sakatarensa na kasar. Andrew ya fusata kwarai kuma ya soki zaben da sakamakon zaben a matsayin “cinikin cin hanci.”

KU KARANTA KUMA: Shin Soyinka zai yaga katinsa na zama a Amurka

2. Samuel Tilden (1876)

Shugabannin Amurka guda 4 da suka samu yawan kuri'u
Samuel Tilden da Rutherford Hayes

An gudanar da zaben shugabancin kasar Amurka na shekara 1876 a ranar Talata, 7 ga watan Nuwamba, 1876 kuma ya zamo daya daga cikin zaben shugabanci mafi husuma da rigima a tarihin kasar Amurka.

Sakamakon zaben ya kasance daga cikin mafi jayayya da aka taba yi, saboda Samuel J. Tilden na birnin New York ya samu yawan kuri;u fiye da Ohio’s Rutherford B. Hayes a kuri’un da sukayi fice. Bayan kirgan kuri’u na farko, Tilden ya lashe kuri’u 184 Hayes kuma 165, tare da kuri’u 20 da ba’a warware ba.

An yi wata yarjejeniya don warware matsalar: kuri’u 1877 da ake jayayya akai, wanda y aba dukkan kuri’un zaben guda 20 ga Hayes. Don haka an kaddamar da Hayes a matsayin wanda ya lashe zabe da kuri’u  185.

3. Grover Cleveland (1888)

Shugabannin Amurka guda 4 da suka samu yawan kuri'u
John Quincy Adams da Benjamin Harrison

An gudanar da zaben shugabancin kasar Amurka na shekara ta 1888 a ranar Talata, 6 ga watan Nuwamba, 1888.

Grover Cleveland ya kasance shugaba mai ci kuma Democrat, ya kuma yi kokarin dawo wa a zagaye na biyu inda yake takara da dan Republican Benjamin Harrison, wani tsohon sanata na Amurka daga Indiana.

Cleveland ya fadi zabe a kolejin zabe, duk da cewan shi ya ci mafi yawan kuri’a da kadan. Cleveland na da kuri’u 5,443,892, yayinda Harrison ke da 5,534,488 amma Harrison ya dauke jihohi 20 (mazabu), yayinda Cleveland ya dauki 18.

KU KARANTA KUMA: Yan zanga-zanga sun mamaye Abuja kan zaben Rivers

4. Al Gore (2000)

Shugabannin Amurka guda 4 da suka samu yawan kuri'u
George Bush da Al Gore

An gudanar da zaben kasar Amurka na shekara ta 2000 a ranar Talata, 7 ga watan Nuwamba na shekara ta 2000.

Takaran zaben ya kasance a tsakanin Dan takarar Republican George W. Bush da kuma dan takaran Democrat Al Gore, mataimakin shugaban kasa mai ci kuma dan babban dan siyasa Albert Gore, sr.

A karshe, Al Gore ya samu kuri’u 50,999,897, fiye da Bush dake da 50,456,002, amma duk da haka Bush ya lashe mazabu 30 yayinda Gore ya lashe 20 don haka ya fadi zabe yayinda Bush yayi nasara.

Wannan misalai ya nuna cewa yawancin lokuta wanda yayi nasarar lashe zabe baya nufin yawan mutanen da suka zabe shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel