Farfesa Wole Soyinka yace Najeriya da Afrika sun bani

Farfesa Wole Soyinka yace Najeriya da Afrika sun bani

- Farfesa Wole Soyinka bai ji dadin nasarar Donald Trump ba a zaben Kasar Amurka

- Mashahurin Farfesan yace a dakata da maganar keta katin sa da yayi alkawari

- Donald Trump dai ya ci zaben Shugaban Kasar Amurka, Wole Soyinka yace Najeriya za ta shiga wani hali

Farfesa Wole Soyinka yace Najeriya da Afrika sun bani
Wole Soyinka

 

 

 

 

 

 

 

Sanannen Farfesan nan, Wole Soyinka yace Najeriya za ta samu kan ta a cikin wani hali bayan nasarar Donald Trump a zaben Amurka. Farfesa Wole Soyinka yace Najeriya da sauran Kasashen Afrika musamman na Yamma ba za su rika samun irin taimakon da suka rika samu a lokacin Shugaba Barrack Obama ba.

Wole Soyinka yace Donald Trump na hawa mulkin Kasar zai ce ai babu dalilin Amurka ta ba Afrika gudumuwa, don a nasa tunanin, ba aikin Amurka bane wannan. Najeriya da sauran Kasashen Yammacin Afrika sun samu gudumuwa na sama da Dala Miliyan 70 na sayen makamai da horon Soji a mulkin Obama. Wole Soyinka yace, an yi ta an gama da hawan Trump.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya hana kama babbar kujera a jirgi

Farfesa Wole Soyinka yace sai da yayi nesa da Talabijin lokacin zabe, har sai jiya da safe, yayin da aka sanar da cewa Trump yayi nasara. Farfesan yace ya ji duk ya rasa inda zai sa kan sa don bakin ciki.

Wole Soyinka da yace da wuya Trump yaci zabe, yace idan ma yaci, to zai bar Kasar Amurka. Zai yi wahala Donald Trump yaci zabe, abu ne mai wahalan gaske kwarai, cewa Soyinka a kwanakin baya.

 

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel