Tsohuwa ta ba Buhari Akuya

Tsohuwa ta ba Buhari Akuya

- Wata tsohuwa ta yiwa shugaba Muhammadu Buhari kyautar Akuya a yayin ziyarar aiki da ya kai jihar Edo

- Tsohuwar ta ce ta yi hakan ne saboda kaunar shugaban ga talakawansa ta hanyar yadda yake gudanar da mulkinsa

Tsohuwa ta ba Buhari Akuya

Wata tsohuwa a jihar Edo ta yiwa Shugaba Buhari kyautar bazata a yayin ziyarar aiki na kwanaki biyu da shugaban ya kai a jihar Edo.

Dattijiwar mai yawan shekaru mai suna Garace Egbon ta yiwa shugaba Buhari kyautar Akuya ce a ranar 7  ga watan Nuwamba a yayin bikin bude Kwalejin Ilimi na Samuel Ogbemudia  a Benin babban birnin jihar.

Tsohuwar wacce ‘yar fansho ce, kuma ‘yar jam’iyyar APC daga mazaba ta 7 a karamar hukumar Oredo, ta ce, ta yiwa shugaban wannan kyauta ne akuya domin nuna kauna ga shugaban da kuma yadda yake tafi da mulkin kasar domin amfanin talakawa.

Wani jami’in gwamnati da ya ki ya bayyana sunansa, wanda kuma ya shaida al’amarin ya ce: “Tsohuwa Grace ta yi ta maza a inda ta keta taron jama’ar da ke wurin, ta kutsa ta kuma nufi inda shugaban ya ke a daidai lokacin da ya gama abin da ya ke yi, ya kuma nufi motarsa dauke da akuya.”

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa ya kaddamar da ayyuka a jihar Edo (Hoto)

Duk da cewa Garace ba ta samu mikawa shugaban kyautar hannu da hannu ba, majiyar ta cigaba da cewa, gwamna Oshiomhole ne ya karbi akuyar a madadin shugaban, ya kuma gode mata da wannan halin girma, sanna ya kuma mikawa jama’in  fadar gwamnatin jihar.

Sai dai ba’a sani ba ko sakon ya kai ga shugaban ko a’a,  amma wannan hali na tsohuwa Grace ya zo daidai lokacin da wasu ke zagin shugaban dangane da halin da kasar ta ke ciki, da kuma salon mulkinsa.

Idan za’a iya tunawa a lokacin yakin neman zabensa a shekarar 2015 wata tsohuwa daga jihar Kebbi ta ba Buhari gudunmawar kudin masu yawa da ga sana’arta na sayar da abinci saboda kauna.

Hakika idan wani da ya ki ka da kwana, wani da shekara ya ke nemanka, aiko mana da ra’ayinku kan wannan labari na kyautar akuya a shafinmu na Facebook.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel