Murnar zaben Trump a Maiduguri

Murnar zaben Trump a Maiduguri

-Yayin da cikin musulmai musamman wadanda ke Amurka ya duri ruwa a sakamakokn cin zaben Donald Trump, a Maiduguri murna a ke yi  da farin ciki

-Mutanen Borno na murna ne a bisa hasashen cewa sabon shugaban zai taimaka matuka wajen ganin bayan ‘yan ta’addan Boko Haram

Murnar zaben Trump a Maiduguri

 Wasu mazauna garin Maiduguri babban birnin jihar Borno sun kwana cikin farin ciki da murnar lashe zaben Donald Trump na zama shugaban Amurka.

A cewar wani rahoton kamfanin dillancin labarai na Nigeria NAN, mazauna Maiduguri sun nunan gamsuwarsu kuma cike da murna da sakamakon zaben da ya ba Trump nasara kan abokiyar karawarsa Hillary Clinton a zaben da aka gudanar farkon makon nan.

A hirar da NAN ya yi da wasu mazauna garin, sun ce sandiyyar murnar ta su ita ce, sabon shugaban zai taimaka wajen kawo karshen ‘yan ta’addan BokoHaram, daya daga cikinsu shine Muhammad Ibrahim, wani ma’ikacin gwamnati a jihar ke cewa, yana murna da samun nasarar Trump saboda hakan zai kawo karshen ta’addanci a Nigeria, “Hakika karshen Boko Haram ya zo, saboda (Trump) yayi alkawarin ganin bayan kungiyar ISIS wanda ke daukar nauyin su.”

Shi kuwa Abba Kyari cewa ya ke yi, sabon shugaban na Amurka zai kawo karshen karayar tattlin arzikin Nigeria ne, saboda manufofin gwamantinsa zai sa farashin Mai a kasuwar duniya ya hau, hajkan kma riba ce ga Najeriya, zai kuma kawo karshen karyar tattalin arzikin duniya.

A lokacin yakin neman zabensa dai, Donald Trump ya yayi alkawarin kawo karshen kungiyar ISIS da Boko Haram ke da alaka da ita, baya ga wasu alkawarurruka da ya dauka na kawo wasu muhimman sauye-sauye a manufofin gwamnatin Amurka.

An dade ana zargin cewa, Amurka da taka rawa wajen barnar da Boko Haram ke yi a Najeriya a lokacin Hillary Clinton tana rike da mukamin Sakatariya tsaro, domin ta hana sayarwa da kasar makamai na zamani.

Sannan cikin wasu abubuwan da aka fallasa na Hillary da Obama shi ne ba kungiyar ISIS taimakon ta bayan fage, wasu ma na cewa su suka ta kirkireta domin cimma wata manufa ta siyasar duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel