Abubuwa 5 game da Abu Ali

Abubuwa 5 game da Abu Ali

Hukumar Legit.ng ta yi wata hira da wasu manyan yan kasuwa dake siye da siyarwa a babban kasuwar nan ta masalacin Juma’a dake Agege, jihar Lagas.

Abubuwa 5 game da Abu Ali
Laftana Kanal Abu Ali

Wannan hira ta bamu damar jin ra’ayinsu game da babban jami’in sojan nan, Laftana kanal Muhammad Abu Ali wanda yan kungiyar Boko Haram suka kashe a ranar Juma’a 4 ga watan Numaba, a karamar hukumar Mallam Fatori dake jihar Borno.

Sun kuma yi masa addu’oi da kuma mika ta’aziyarsu ga iyalamn marigayin.

Ga muhimman abubuwa guda 5 da suka fada a kan marigayin:

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 10 da Donald Trump ya fada bayan zaben Amurka

1. Mutun ne jan gwarzo kuma jarumi

Ya kasance namiji jan gwarzo wanda baya kallon matsayin da ya kai a bakin komai. A matsayinsa na babban jami’in soja zai iya tura kananan jami’an dake karkashinsa yana kwance a gida, amma shi baya haka tare da shi ake zuwa filin daga. Mutun ne mai kokari da himma.

Abubuwa 5 game da Abu Ali
Laftana Kanal Abu Ali

2. Kasar Najeriya tayi babban rashi

Babu shakka samun jarumi soja mai nagarta da kokari irin sa zai yi wuya, domin ya sadaukar da kansa don ganin ci gaban kasar da kuma kore duk ayyukan ta’addanci dake kawo farmaki da barazana ga kasar.

Abubuwa 5 game da Abu Ali
Gawan marigayi Abu Ali

3. Yan Najeriya na tsananin bakin ciki

Munji bakin ciki fiye da yanda ake zato domin ya kasance mutun ne mai kokari wanda ke taimako da kishin kasa sosai, ya jajirce gurin kokarin ganin sunyi nasarar ceto garuruwan da yan Boko Haram suka mamaye.

Abubuwa 5 game da Abu Ali
Marigayi Abu Ali a bakin aiki

4. Ya kasance madubin dubawa

Kanar Muhammad Abu Ali ya kasance jami’I mai tawakkali da taimakon sauran sojojin Najeriya ta hanyar karfafa masu gwiwa, da kuma basu shawara kan hanyoyin da zasu yakin yan ta’addan Bko Haram ba tare da tsoro ko shakku ba.

Abubuwa 5 game da Abu Ali
Ya kasance Gwarzo a lokacin da yake raye

5. Gwamnati ta lura da iyalinsa

Ya kamata gwamnatin tarayya da masu hali su lura da iyalinsa domin ya sadaukar da kansa ga kasar. Ya kuma cancanci a saka masa ta hanyar duba iyalinsa, kada a bari su taggayara domin suna cikin wani hali a yanzu wanda Allah kadaine zai kasance gatansu.

Abubuwa 5 game da Abu Ali
Abu Ali tare da iyalinsa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel