Yan kasuwa 3 a Najeriya da zasu yi koyi da Donald trump

Yan kasuwa 3 a Najeriya da zasu yi koyi da Donald trump

- Yanzu haka dai kura ta fara lafawa a kasar Amurka bayan da hamshakin dan kasuwar nan kuma mai kudin gaske Donal Trump ya samu nasarar zama shugaban kasar Amurka na 45. Wannan dai ya jefa kusan duka duniya a cikin rudani da halin dar-dar da rashin tabbas

- Shi dai Trump mai shekaru 70 ya gina kasuwancin sa ne ta hanyar gine gine da sauran su

Kamar Donald Trump, a Najeriya ma akwai yan kasuwa da dama da ba kasafai sukan shiga siyasa ba amma kuma suna da matukar kwarewa a harkokin su na kasuwanci. Mafi yawancin su babbar damar da sukan samu bata wuce mukami ba a cikin gwamnatin da wani wanda bai kai su kwarewa ya kafa ba.

Yanzu dai nasarar da Donald Trump din ya samu na zaman kamar wani kalubale ne ga wasu manyan yan kasuwar mu na Najeriya.

1. Tony Elumelu

Yan kasuwa 3 a Najeriya da zasu yi koyi da Donald trump
Tony Elumelu

Yana da matukar sa'a a kasuwanci. Tun yana dan shekara 34 ya shugaban ci bankin Standard Trust inda ya kuma yi nasarar maida da babban banki cikin dan kankanin lokaci. A shekara ta 2005 kuma ya jagoranci wani shirin hadaka da bankin nashi da UBA wanda yanzu haka yake da rassa a kusan kasashe 18 a nahiyar Afrika.

Yana da matukar kwarewa a harkar gudanar da mutane sannan yana da ilimi sosai. Tabbas ya kamata ya gwada shiga siyasa.

Ku Karanta kuma: Banbancin zaben kasar Amurka da kuma Najeriya

2. Jim Ovia

Yan kasuwa 3 a Najeriya da zasu yi koyi da Donald trump
Jim Ovia

Shima dai wannan yana da kwarewa sosai. Ovia yana da kwarewa ta sama da shekaru 23 a harkar banki. Tare da shi aka kafa bankin Zenith a shekara ta 1990 sannan kuma ya shugabance shi har zuwa 2010. Yana kuma da kwarewa sosai a harkar sadarwar zamani inda yanzu haka ya mallaki jami'ar sadarwar zamani dake garin Agbor, jihar Delta.

Yadda duniya ke juyawa ya zuwa harkar sadarwar zamani, ko shakka babu zai bada muhimmiyar gudummuwa wurin tabbatar da faruwar hakan amma idan har zai shiga siyasa.

3. Aliko Dangote

Yan kasuwa 3 a Najeriya da zasu yi koyi da Donald trump
President of Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote

Yo ai ko ma ba'ace komai ba kowa yasan Dangote. Shine wanda yafi kowa kudi a nahiyar Afrika. Masana na cewa yanzu dai kam lokaci yayi da yakamata ya dena yin siyasa a bayan fage yafi to yayi ta karara. Ko shakka babu yana da kudin da kuma basirar kai har ma da duk wani abu da dan siyasa zaiyi tinkaho dashi.

Tarihi dai ya nuna cewa ya fara kasuwancin shi ne da bashin N500,000 da ya samu daga wurin kawunsa a shekara ta 1977.

https://youtu.be/KhUBU4G1n0U

Asali: Legit.ng

Online view pixel