Toni din Real Madrid zai yi jinya mai tsawo

Toni din Real Madrid zai yi jinya mai tsawo

- Likitocin Real Madrid sun tabbatar da cewar dan kwallon tawagar Jamus, Toni Kross, ya yi rauni.

- Dan kwallon ya yi rauni ne a karawar da Madrid ta ci Leganes 3-0 a ranar Lahadi a gasar La Liga da suka fafata.

- A makon jiya ne, Toni Kross, ya sabunta yarjejeniyarsa da Real Madrid domin ci gaba da buga mata tamaula zuwa 2022.

Toni din Real Madrid zai yi jinya mai tsawo
masu wasan kwallon kafa

Dan kwallon mai shekara 26, wanda ya koma Bernabeu daga Bayern Munich a shekara 2014, ya ci wa Madrid kwallaye hudu a wasanni 108 da ya buga mata.

KU KARANTA: Za'a sake tuhumar Neymar da Barcelona

A wani labarin kuma, Cristiano Ronaldo ya ce zai iya ci gaba da taka leda a kungiyar zuwa shekara 10, idan yarjejeniyar da ya sake kullawa da kungiyar ta kare.

Kwantiragin Ronaldo mai shekara 31, da Real Madrid na shirin karewa a watan Yunin 2018, amma ya tsawaita ta, inda zai kai karshen kakar wasan 2021.

Dan kwallon na tawagar Portugal ya ce ba wannan ba ne karo na karshe da zai tsawaita yarjejeniyar ci gaba da wasa a Madrid, yana fatan sai ya kai shekara 41 kafin ya yi ritaya.

Ronaldo ya ci kwallaye 371 tun lokacin da ya koma Madrid da taka-leda daga Manchester United a shekarar 2009.

https://youtu.be/KhUBU4G1n0U

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel