Ma'aurata sun haifi tagwaye bayan shekaru 15

Ma'aurata sun haifi tagwaye bayan shekaru 15

Zai iya zama karayar zuciya ga Ma’aurata idan suka dauki lokaci mai tsawo da yin aure ba tare da samun haihuwa ba.

Wani mutumi mai suna Chux Obusom, ya fito yana godiya ga ubangiji da ya albarkace su da samu tagwaye shi da matarsa bayan sun dauki tsawon shekaru goma sha biyar suna jiran tsammani.

Ma'aurata sun haifi tagwaye bayan shekaru 15

A wani rubutu da aka buga a shafin zumunta na Facebook, Obusom ya yada hotunan sababbin yaransa dauke da rubutu kamar haka, “Ubangiji da baya taba karya ko rashin cika alkawari ya albarkaci iyalina da haihuwar tagwaye: namiji da mace bayan mun dauki tsawon shekaru 15 muna jira. Shi kadai ne abun yabo.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 10 da Donald Trump ya fada bayan zaben Amurka

Rubutun ya samu ra’ayin jama’a sama da 580 da kuma wadanda suka kuma yada hotunan sama da 260 wannan ne ya jawo hankulan mutane da dama wadanda suka tura sakon taya murna da godiya ga ubangiji bisa ga ni’imar da yayi wa rayuwarsu.

Ma'aurata sun haifi tagwaye bayan shekaru 15

Lallai wannan abu ya cancanci murna ga ma’aurata ko me kuke tunani?

Asali: Legit.ng

Online view pixel