Ana binciken Amaechi akan kwangilan titin jirgin $2 billion

Ana binciken Amaechi akan kwangilan titin jirgin $2 billion

- Majalisan dattawan Najeriya ta tuhumci yadda akayi cinikin titin jirgin da ministan sufuri Rotimi Amaechi yayi

- Majalisar dattawa tace  Amaechi ya sabawa dokan public enterprises Act, 1999

Ana binciken Amaechi akan kwangilan titin jirgin $2 billion

Majalisar dattawa ta ce Rotimi Amaechi ya saba doka wajen cinikin ginin titin jirgi

Majalisar dattawan ta yanke shawaran cewa zata binciki ministan Sufuri ,Amaechi akan laifin bin hanyar da ya kamata wajen cinikin hantar Fatakwal- Maiduguri da Legas-Kano ga kamfanin Amurka.

KU KARANTA: Matar da ta raba abinci a jahar Legas ta zamo tauraruwa

Jaridar Premiuim Times ya ruwaito a wata hiran da Amechi yayi da CNBC a watan yuni inda yace Najeriya ta yi ciniki da kanfanin GE wajen gina titin jirgin ksa Legas zuwa Kano da kuma Fatakwal zuwa Maiduguri kimanin kudi $2 Billion.

Amma, majalisar dattawa a ranan talata,8 ga watan Nuwamba a wata kara da Akpan Bassey  ya shigar na usulubin da aka bi wajen cinikin gina titin jirgi da kamfanin GE cewa Amaechi ya saba dokar Najeirya na yin cikin da kansa.

Sanata Bassey, wanda yake shugaban kwamitin majalisar dattawa akan isakan gas, yace a lokacin da aka tabbatar da aikin a Afrilun 2015, cibiyar aikin jama’a sun shirya wata hanya na kaddamar da aikin jirgin.

 

Zake tuna cewa Alkalan kotun koli guda 2 sun tuhumce Amaechi cewa yana son suyi cuta wajen alkalanci domin baiwa APC nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel