Hoton ginin Abu Ali da Boko Haram sun kashe

Hoton ginin Abu Ali da Boko Haram sun kashe

Hoton gaban ginin da jajirtaccen soja lt.kanal Ali Muhammad Abu da yan kungiyar boko haram suka kashe a jahar Borno, Maiduguri. 

Hoton ginin Abu Ali da Boko Haram sun kashe

Jajirtaccen sojan da wasu sojoji guda 4 an kashe su ranar juma'a da yamma 4 ga watan Nuwamba a yayin musayar wuta da suka yi da yan kungiyar boko haram" kakakin sojoji  Kanal Sani Usman ya bayyana faruwar lamarin.

Ali ya rasu in da ya bar yawan cin yan Najeriya da jimami wanda har ya hada da shugaba Buhari, wanda har ya bayyana shi a matsayin jarumi jajirtaccen soja kuma komanda wanda ba tura wa yake kawai ba, har da shi ake fuskantar abokan gaba duk hadari kuma duk rintsi.

Sai dai wasu yan Najeriya sun caccaki shugaba Buhari kan halin ko in kula na kin sama sojojin mu kwarin guiwa wadanda suke yaki da yan ta'adda.

Wasu yan Najeriya sunce ana bukatar Buhari da yayi abun da ake bukata ya kuma ziyarce su a yankin dan ze kara masu kwarin guiwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel