Rundunar sojin sama sun tare wata harin Boko Haram

Rundunar sojin sama sun tare wata harin Boko Haram

– Hukumar sojin saman Najeriya ta kawar da wata harin da Boko Haram ta kawo ma sojin kasa

– Kana jiragen yakin sama sun kai hare-hare dare da rana

Rundunar sojin sama sun tare wata harin Boko Haram

Jirgin yakin saman rundunar sojin saman Najeriya ta kawar da wata harin da yan kungiyar Boko Haram suka kai wa rundunar sojin kasa a Kangarwa a jihar Barno.

Ayodele Famuyiwa, kakakin rundunar sojin saman, ya bayyana hakan ne a wata jawabi a ranan litinin, 7 ga wtan Nuwamba.

KU KARANTA: Rundunar soji sun saki mutane 1271 da ake wa zargin Boko Haram Maiduguri

Jawabin tace: “Bayan jirgin yakin sama ta kawar da wata harin yan boko haram, an aika jirgin leken asiri ta taimakwa rundanar sojin kasa wajen gano inda yan ta’addan suke. Farnakin da aka fara misalign kar 5 na yamma zuwa karfe 7:15 na dare kafin aka samu kawar da su ga ba daya.

Famuyiwa yace, kafin wannan m a Kangarwa, rundunar ta kai wasu hare-hare a ranan 6 ga watan Nuwamba.

Ya kara da cewa an kai hare-hare Kashimeri, Tumbu Gini, chukugudu da su wurare inda suka kai hari Bama. An samu labarin cewa na birne wannan jarimin oa Lt Col Abu Ali a  Abuja.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel