An ci gaba da shari'ar Saraki

An ci gaba da shari'ar Saraki

Biyo bayan watsi da bukatar da ya gabatar dangane da shrai’ar da a ke yi masa, shugaban majalisar dattawa Bukola Abubakar Saraki kan bayyana karya wajen bayyana kadarorinsa ya ci gaba a ranar Litinin 7 ga watan Oktoba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

An ci gaba da shari'ar Saraki
Saraki a zauren majalisar dattijai

Legit.ng samu labarin cewa hakan ya samar da wani yanayi maras  dadi a Majalisar dattijan , wanda shi Sarakin ke jagoranta. An ci gaba da sauraron karar karkashin alkalin kotun Danladi Umar.

Rahoton ya ci gaba da cewa, za’a ci gaba da fuskantar shari’a  karkashin kotun kyautata da’ar ma’aikata, kudurin da Sarakin ya nema na shugaban kotun ya cire kansa daga sauraron karar bai sami shiga ba a ranar 5 ga watan oktoba.

KU KARANTA KUMA: Shugabannin Majalisa sun lankwame biliyan 10 –Jibrin

Kotun daukaka karar da ke Abuja ta yi watsi da bukatar Saraki inda ta tabbatarwa da kotun ta da’ar ma’aikata damar cigaba da yin masa shari’a.

Rahoton ya ci gaba da cewa, za’ a ci gaba da sauraron karar a inda shaida na farko zai fuskanci tambayoyi, Michael Wetkast,  jami’I daga hukumar yaki da cin hanci da yi wa tattali arzikin kasa zako kasa EFCC, wanda ya bayyana abubuwa masu yawa agame da case din.

Kwamiti koli da kuma majalisar dattawa sun dade cikin kawancen mage da bera, a kusan wurare guda biyu, majalisar dattawan suna ganin baiken mulkin na shugaba Muhammadu Buhari.

Kotun daukaka karar da ke Abuja ta yi watsi da bukatar Saraki inda ta tabbatarwa da kotun ta da'ar ma’aikata damar ci gaba da Shari'arsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel