Bana zuwa gayyar sodi, inji Bafarawa

Bana zuwa gayyar sodi, inji Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa ya bayyana dalilin daya sa ba’a ga keyarsa a taron bikin cikar mai alfarma Sarkin Musulmi shekaru 10 a karagar mulki ba.

Bana zuwa gayyar sodi, inji Bafarawa

Bafarawa yace babu wanda ya gayyace shi bikin, don haka ba zai je gayyar sodi ba, inji rahoton jaridar Dailu Trust.

Bafarawa ya nuna bacin ransa da rikon sakainar kashin da aka yi masa tab akin Sakataren watsa labarai na jam’iyyar PDP Yusuf Dingyadi yace “har zuwa ranar da aka fara hidindimu bikin, ba’a kawo ma mai girma Attahiru Bafarawa takardan gayyata ba.

“tun kusan sati daya da bikin ya dawo gida daga Abuja da tunanin zai aika masa da takardar gayyata a matsayinsa na mai rike da sarautar garkuwar Sakkwato, wanda kuma shi daya tilo yayi kokarin har ya tabbatar da nadin mai alfarma Alhaji Sa’ad Abubakar a matsayin Sarkin musulmi bayan rasuwar yayansa, a zamanin yana Gwamna.”

KU KARANTA: Buhari baya jin magana - Bafarawa

A cewarsa, da gangan ne aka ki gayyatan Bafarawa don a hana shi tabuka wani abu a bikin gaba daya. Dingyadi ya cigaba da cewa don haka ne Bafarawa ya kaurace ma taron don gudun kawo matsala a taron. Daga karshe yace duk da share shi da aka yi, ba zai gaza ba wajen kokarin daya saba na ganin ya ciyar da masarautar Sakkwato da jihar gaba daya gaba.

A zamanin gwmanatin Bafarawa ne aka nada mai alfarma Sarkin Musulmi a shekarar 2006 don ya gaji yayansa marigayi Muhammadu Maccido wanda ya rasu a hadarin jirgin sama a filin tashin jirgin sama na tunawa da Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Taron daya gudana a ranar Asabar 5 ga watan Nuwamba ya samu halartan manyan mutane ciki har da shugaban kasa Muhammadu Buhari, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki, da sauran manyan mutane.

 

&index=40&list=PL6sEiOi0w1ZCJ2pYczvQeEWNY5u811xJt

Asali: Legit.ng

Online view pixel