Karanta banbancin zaben Amurka da Najeriya

Karanta banbancin zaben Amurka da Najeriya

- Amurkawa na shirin zaben sabon shugaban kasa da zai gaji Barack Obama tsakanin Donald Trump na Jam’iyyar Republican da Hillary Clinton da Democrat. Ko ya tsarin zaben Amurka ya ke? 

- Ana zaben Shugaban kasa ne duk bayan shekaru hudu a Amurka a ranar Talata bayan Litinin din farkon watan Nuwamba. Zaben 2016 ya fado ne a ranar 8 ga watan Nuwamba.

Karanta banbancin zaben Amurka da Najeriya
The government building (pictured after the shooting) is just meters away from the White House

Amurkawa na fara jefa kuri’a tun kafin ranar zabe. Sai dai kuma kuri’iun da aka kada ba su ke tantance wanda ya lashe zaben ba.

Yawan Jama’ar da Dan takara ya samu fiye da abokin takara ba shi ke tantance ya lashe zaben ba, akwai wata Majalisar wakilai masu kada kuri’a daga jihohin Amurka 50 da ake kira Electoral College da yawansu ya kai 538. Kafin dan takara ya lashe zaben sai ya samu kuri’u 270 daga kuri’un majalisar wakilan.

Yawan kujerun Majalisar sun banbanta tsakanin Jihohi, domin wata Jihar tana da 20 saboda yawan jama’arta wata kuma tana da kujeru uku kamar yadda ake raba wakilci a Majalisar Wakilai da ta Dattijai tsakanin Jihohin Amurka. Kuma ana zaben wakilan Electoral College ne daga manyan Jami’an jihohi ko kuma jiga-jigan Jam’iyyun siyasa.

KU KARANTA: Karanta kyayyawan tsarin da gwamnatin shugaba Buhari yayi ma matasa

Duk dan takarar da ya samu yawan wakilan da suka zabe shi a Jiha shi ne ya lashe zaben kuri’un da al’umma suka kada.

Akwai manyan jihohi biyar masu muhimmaci da suka hada da Florida da North Carolina da Ohio da Pennsylvania da Texas da ke tantance makomar sakamakon zaben Amurka. Amma sauran Jihohin na iya tasiri idan har ‘Yan takara na da tabbacin samun kuri’u 270 daga masu kada kuri’a a Majalisar wakilai.

Dan takara na iya samun rinjayen Kuri’un Jama’a kuma ya fadi zaben.

Hakan ta taba faruwa a zaben 2000 inda Al Gore ya samu kuri’un Jama’a fiye da George W. Bush, amma ya fadi zaben saboda Bush ya fi shi samun kuri’un masu jefa kuri’a a majalisar wakilai da ake kira Electoral College. A Jihar Florida ne a lokacin, daya daga cikin manyan Jihohin Amurka aka tantance sakamakon zaben.

https://youtu.be/KhUBU4G1n0U

Asali: Legit.ng

Online view pixel