Sojoji sun mayar wa da yan Boko Haram martani

Sojoji sun mayar wa da yan Boko Haram martani

- Dakarun sojojin Nijeriya dake garin Kangarwa a karamar hukumar Kukawa dake jihar Borno sun yi nasarar kashe 'yan Boko Haram guda 13 a yayin wata farauta da suka fita, inda wasu daga cikin 'yan Boko Haram din da dama suka tsira da harbin bindiga.

- Saidai soja daya ya rasa ransa a yayin artabun, yayin da guda uku suka samu rauni.

Sojoji sun mayar wa da yan Boko Haram martani
The Nigerian military is swooping down on Sambisa forest to destroy the terrorists

Sojojin sun kuma yi nasarar karbe makamai da motacin 'yan bindigan a yayin artabun wanda aka dauki tsawon awanni hudu ana fafatawa.

A jiya ne dai hukumomin sojin Najeriya suka gudanar da jana'izar kwamandan rundunar sojin kasar ta 272 mai kula da tankokin yaki, Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, tare da wasu sojoji hudu.

Kwamandan da sauran sojojin hudu sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke kokarin dakile wani harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai kan barikin sojin kasar na 119 da ke garin Malam Fatori a Jihar Borno.

Haka ma wasu sojojin hudu sun samu raunukka yayin da mayakan Boko Haram 14 suka halaka a cikin artabun na yammacin ranar Asabar.

A shekara ta 2015 ne Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi wa Muhammad Abu-Ali karin girma daga Manjo zuwa Laftanar Kanar tun kafin ya kai shekarun samun karin girman, saboda jaruntar da ya nuna da ta kai ga kwato yankuna da dama daga hannun mayakan na Boko Haram.

Karshen satin da ya gabata ne dai Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, tare da wasu sojojin hudu, lokacin da suka dakile wani harin mayakan Boko Haram a kan barikin sojin kasar na 119 dake Mallam Fatori, jihar Borno.

Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, shi ne kwamandan runduna ta 272 mai kula da tankokin yaki.

Saboda jarumtarsa ne, a 2015 a Gamboru Ngala, babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya yi mushi karin girma daga Manjo zuwa Laftanar Kanar tun kafin ya kai shekarun samun karin girman.

Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin kasa ta kasar, Kanar Sani Uman Kukasheka, ya ce sojojin sun kashe mayakan Boko Haram din goma sha hudu a lokacin artabun.

Ya ce wasu sojojin hudu kuma sun samu raunuka a harin wanda mayakan kungiyar suka kai a daren Juma'a.

Kanar Kukasheka ya ce cikin makaman da sojojin suka kwace daga wurin mayakan sun hada da babbar bindiga samfurin GPMG, da AK-47 guda bakwai da kuma albarusai da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel