An lakada ma wani Soja duka a Warri

An lakada ma wani Soja duka a Warri

Wani jami’in Soja da ba’a bayyana sunan sa ba ya ci na jaki a hannun jama a ranar Litinin 7 ga watan Nuwamba bayan an zarge shi da satar waya salula a garin Warri.

An lakada ma wani Soja duka a Warri

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewar hatsaniyar ta samu asali ne bayan wata budurwa ta saka ihun barawo a wani babban shago mai sun ‘Robson G Shopping Plaza’ dake titin Okumagba Avenue bayan ta gane Sojan daya taba mata fashin wayar salula. Daga nan ne jama’a suka bi shi a guje, inda bayan sun kama shi suka lakada ma dukan kawo wuka, sai da kyar yansanda suka kwace shi.

Rahoton jaridar Daily Post ya cigaba da cewa yansanda sun wuce da barawon zuwa gidan tsohon babban hafsan sojan kasa Manjo Janar David Ejoor don su tabbatar da sahihancin ikirarin da yake yin a cewa shi Soja ne. daga nan sai sojojin dake gadin gidan suka tarwatsa jama’an, kuma suka ki mika shi ga yansandan.

An lakada ma wani Soja duka a Warri
Rigar sojan bayan yaci duka

Bayan wani dan lokaci sai wata motar Sojoji ta wuce da shi zuwa barikin soja na bataliya ta 3 dake garin Effurun. Sai dai majiyar Daily Post ta bayyana cewa Sojan ya daku, kuma an ji masa ciwo, don haka an kwantar da shi a asibiti.

KU KARANTA:Yayi ma matarsa duka kan tana dawowa gida latti daga aiki

An lakada ma wani Soja duka a Warri
Jama'a suna jira a kofar gidan Janar Ejoor

Majiyar tace “bamu samu damar yi ma sojan tambayoyi ba, sakamakon raunukan daya samu daga duka, don haka mun mika shi asibiti.”

An lakada ma wani Soja duka a Warri
Motar Sojojin data gudu da sojan

A wani labara kuma, an samu cikakken bayani dangane da yadda aka kashe Jarumi laftanar kanar Muhammad Abu Ali tare da abokan aikinsa 6 a bakin daga a jihar Borno. Kaakakin rundunar soja Kanal Usman Kukasheka ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar.

&index=72&list=PL6sEiOi0w1ZCmg6rIvhdW7Xeicx_0Gk05

Asali: Legit.ng

Online view pixel