Ku karbi lambobin makiyaya a jihohinku

Ku karbi lambobin makiyaya a jihohinku

- Kungiyar makiyayan Najeriya, Miyetti Allah sun bukaci yan Najeriya da su karbi lambobin wayar makiyaya a jihohinsu

- Shugaban kungiyar ta Miyatti Allah a jihar Abia, Hassan Buba yace dukkan mambobin garin su tabbatar suna da lambobin wayar makiyaya a jihar

- Ya ce samun wadannan lambobin zai taimaka wa mazauna garin duba mamayewar makiyaya a yankinsu

Ku karbi lambobin makiyaya a jihohinku
Fulani makiyayi

Kungiyar makiyayan Najeriya wato Miyatti Allah sun bukaci yan Najeriya da su karbi lambobin  wayar makiyaya a jihohinsu.

Da yake Magana a karamar hukumar Obingwa dake jihar Abia, shugaban makiyaya na jihar Hassan Buba yace dukkan mambobin garin su tabbatar sun karbi lambobin wayar makiyaya a jihar.

A lokacin wani ganawa da manyan masu ruwa da tsaki na jihar Buba ya ce wannan zai taimakawa yan garin duba mamayewar makiyaya a yankinsu.

KU KARANTA KUMA: Da Muhammad Abu Ali da sauransu sun tsere ma matuwa

Ya kuma ce kokarin zai taimaka gurin duba barnan da makiyaya sukayi a gonaki da albarkatun gona.

Buba ya kuma roki al’umman garin da su sanar da shugabannin kungiyar a jihar idan dabbobi sunyi wani barna domin sassanci cikin lumana a maimakon tada rikici wanda zai dada tabarbare halin da ake ciki.

Da yake maida martanin sa, shugaban gargajiya na Etiti Ohanze, Eze Marshal Ogbonna ya soki lalata gonakai da albarkatun gona da makiyaya ke yi.

Shugabannin sunyi kira ga jami’an tsaro da kuma shugabannin makiyaya da su duba al’amarin dake tashe.

Jami’in dan sanda na sassan, sashin gabashin yankin, Saleh Musa, yace anyi ganawar ne domin kawo mafita ga karo tsakanin makiyaya da manoma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel