Kalli bidiyon da Buratai ya karrama Gwarzon mayaki Abu Ali

Kalli bidiyon da Buratai ya karrama Gwarzon mayaki Abu Ali

An gano faifan bidiyo dake nuna lokacin da babban hafsan rundunar mayakan sojan kasa laftanar janar Tukur Buratai ke karrama laftanal kanar Muhammed Abu Ali da sabon matsayin.

Kalli bidiyon da Buratai ya karrama Gwarzon mayaki Abu Ali

Shi dai Abu Ali an kashe shi ne a ranar Juma’a tare da abokan aikinsa guda biyu, bayan wata mummunar fafatawa da suka yi da yayan kungiyar Boko Haram, kamar yadda sanarwa daga hukumar soji ta hannun kanal Sani Usman ta bayyana.

Kaakakin rundunar kanal Sani Usman Kukasheka ya bayyana bidiyon a shafinsa na Facebook, inda ya kara da yi ma mamacin addu’a tare da na sauran sojojin da aka yi rashin su.

KU KARANTA:Rundunar mayakan Sojan kasa ta hallaka yan Boko Haram

Kalli bidiyon da Buratai ya karrama Gwarzon mayaki Abu Ali

Yace “ba zamu taba mantawa da wannan lokaci ba, ranar 9 ga watan Satumba a garin Gamboru Ngala, wannan shine lokacin da babban hafsan rundunar mayakan sojan kasa laftanar janar Tukur Buratai, tare da Manjo Janar YM Abubakar (mai rasuwa) suka karrama Abu Ali da shaidar karin girma.

“da fatan Allah jikan Manjo janar YM Abubakar da Laftanal kanar Muhammad Abu Ali da sauran sojojin mu da muka rasa a yayin wannan yaki.” Amin

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel