Har yanzu Buhari yayi shiru akan sunan sabon babban Alkali

Har yanzu Buhari yayi shiru akan sunan sabon babban Alkali

- Akwai tsoron cewa za’a samu gurbi a bangaren shari’a a kwanaki masu zuwa

- Hakan zai iya faruwa ne bisa ga shirun shugaban kasa akn sunan da aka gabatar masa

- Saura kasa da mako daya yanzu babban alkalin Najeiya, Justice Mahmud Mohammed, zai yi ritaya

Har yanzu Buhari yayi shiru akan sunan sabon babban Alkali

Wata rahoton jaridan Thisday ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari har yanzubai amince da sabon babban alkalin tarayyan da aka gabatar da sunan shi ba.

Kuma duk da cewa ana kasa da mako dayam Justice Mahmud Mohammed, yayi ritaya a matsayin babban Alkalin Najeriya.

KU KARANTA: Wajibi ne Buhari ya hukunta masu magudi – APC

Jastis Mahmud Mohammad zai yi ritaya ne a ran Alhamis, inda zai cika shekara 70 a duniya, shekaran da ya zama wajibi ga Alkalan kotun afil da kotun koli suyi ritaya.

A ranan talata,11 ga watan oktoba, majalisar shari’ar tarayya ta gabatar da sunan Jastis Walter Samuel a matsayin sabon Alkalin da ta yarje.

Idan majalisar dattawa ta tabbatar da shi, zai kasance Alkalin Najeriya dan kudanci wanda ya dau mukamin a shekaru 30 da suka gabata. Jastis Ayo Irekefe ne dan kudancin karshe da yah au kujerar a shekarar 1985-1987.

Duk da cewan a doka,bai wajaba shugaban kasa ya yarda da shi ba, amma bashi da hurumin nada wani. Yanada hurumin Magana da NJC cewa a aiko masa da wani suna idan bashi son sunan farko.

Har yanzu dai, majalisar dattawa bata samu wasika daga fadar shuugaban kasa ba akan sabon nadin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel