Wajibi ne Buhari ya hukunta masu magudi - APC

Wajibi ne Buhari ya hukunta masu magudi - APC

- Jam’iyyar APC, shiyar jihar legas tayi gargadin cewa idan fa ba’a hukunta masu magudin zabe, demokradiyya zatayi nisan kiwo

- APC tace tun lokacin da PDP ta dau ragamar mulki a 1999, magudi kara yawaita yakeyi

- APC tace magudi ya kasance babban matsalan zaben da Najeriya ke fuskanta

Wajibi ne Buhari ya hukunta masu magudi - APC
APC Logo

Jam’iyyar APC, shiyar jihar Osun tayi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da yayi amfani hukunci ami tsanani akan masu magudin zabe saboda a ceti demoradiyyan Njaeriya.

Kakakin jam’iyyar jihar, Barr Kunle Oyatomi,a wata jawabin yayi gargadin cea idan ba’a hukunta masu magudi, demokradiyyan najeriya na cikin hadari kuma rashawa zai kashe kasa. Vanguard ta bada rahoto.

KU KARANTA: Abubuwan da suka faru a Najeriya a karshen mako

Kakakin jam’iyyar ya bayar da gargadin ne domin nuna damuwa akan bayanin da ma’aikacin INEC na jihar Ondo Olusegun Agbaje, na cewa wasu jigogin PDP a jihar sunyi shirin basa cin hanci da N500million lokacin da yake jihar Osun a shekarar 2014,saboda yayi magudin zaben jihar.

Mr. Agbaje yak i amsan cin hancin kuma Rauf Aregbesola ya lashe zaben. Duk da cewan APC ta ce magudi ne babban matsalan Najeriya ,y ace tun 1999 da PDP da dau ragamar mulki, magudi na karuwa ne kulln.

“Idan ba’a dau matakai tsattsaura ba, wannan rashawan zai kashe demokrdiyyan mu. Idan masu magudin zabe suna yin abinda suka ga dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel