Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Lt.Kanal Abu Ali

Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Lt.Kanal Abu Ali

- Shugaba Buhari yayi kira da sauran sojin da kada su bari rasuwan Abu Ali ya rage musu karfin guiwa

- “Babban soja ne, ba zamu manta da shi ba. Ya kawo suna mai kyau ga iyalinsa

Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Lt.Kanal Abu Ali
Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa akan rashin kwamandan soji,Abu Ali wanda ya Boko Haram suka kashe a ranan juma’a,4 ga watan Nuwamba.

Jaridar Leadership ta bada rahoton cewa shugaba Buhari,ya bayyana hakan ne ta wata jawabin da mai Magana da yawun, Garba Shehu yayi. Ya siffanta Kanal Abu Ali a matsayin kwamandan da ke da karfin hali,rashin tsoro komin hadari.

KU KARANTA: Yadda Fulani sun hallaka dan uwansu saboda wannan dalili

Kana shugaba Buhari ya yabi mutane irinsa na rundunar soji wadanda suka sadaukar da rayukansu domin tabbatar da cewa kasarmu Najeriya na cikin zaman lafiya.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa marigayi Ali wani babban hafsan soja ne wanda kuma abin so ga mabiyansa,yayi kari da cewan yanada ikon taimakawa wajen fidda tsoro daga cikin zuciya.

A sakon ta’aziyar da Buhari ya aika ga iyalansa da hukumar soji, Shugaban yace sadaukar da ran da suke yi ya wuce abin yabo.

“Babban soja ne, ba zamu manta da shi ba. Ya kawo suna mai kyau ga iyalinsa.

Shugaba Buhari yayi kira da sauran sojin da kada su bari rasuwan Abu Ali ya rage musu karfin guiwa. Yace kada a bari Boko Haram su bata zuciyan sojin mu.

Shugaba Buhari ya sanya wasu manyan ma’aikatan gwamnati karkashin jagorancin Abba Kyari  su wakilce shi a jana’izarsa da za’ayi a yau,litinin 7 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel