Ko Buhari sai da ya gwabza sau 4 Inji Dino Melaye

Ko Buhari sai da ya gwabza sau 4 Inji Dino Melaye

- Sanata Dino Melaye yace yana sa ran wata rana zai zama shugaban kasar Najeriya

- Yace ai ko Shugaba Muhammadu Buhari sai da ya jaraba sau 4 sannan yayi nasara

- Ana nema a ga bayan Saraki, Dino Melaye yace buri a laifi bane

Ko Buhari sai da ya gwabza sau 4 Inji Dino Melaye

 

 

 

 

 

 

 

 

Wani Sanata na Kasar nan yace yana da burin zama Shugaban Kasa wata rana, nan gaba. Sanata Dino Melaye ya bayyana haka ne ga Jaridar Punch a wata hira da suka yi. Dino Melaye yayi magana game da Shugabancin Kasar nan, Majalisa, da wasu abubuwa da dama.

Dino Melaye, Sanata mai wakiltar Yammacin Jihar Kogi yace shi fa burin sa ya zama Shugaban Najeriya wata rana. Sanata Melaye yace bincike Shugaban Majalisar Dattawar Kasar, Dr. Bukola Saraki da ake yi a Kotu, kawai kokarin ganin an ga bayan sa ne. Melaye yace wasu ne kawai ke kai masa hari don yayi takara, yace idan takara laifi ne ai Shugaba Buhari yayi har sau hudu.

KU KARANTA: PDP tace Shugaba Buhari ya kori Amaechi

Sanata Dino Melaye yace sai da Shugaba Buhari ya buga sau hudu sannan ya dace, shima wata ran, zai zama Shugaban Kasa. Dino Melaye yace ba shakka Shugaba Buhari na neman ganin an tsaida sata a Najeriya, amma fa matakan da yake bi, ba dole su zama daidai ba. Don haka yake ganin, za a dade ba a kai labari ba.

Sanata Dino Melaye yace yana ganin ya fi dacewa ace an bada lokaci na afuwa, duk wanda ya saci kudin Najeriya ya maido, shikenan.

KU KARANTA: Mu muka kashe Najeriya-Dino Melaye

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel