Najeriya za ta fara sayan man fetur daga Jamhuriyar Nijar

Najeriya za ta fara sayan man fetur daga Jamhuriyar Nijar

Najeriya da Kasar Jamhuriyar Nijar sun shiga wata yarjejeniyar bunkasa harkar man fetur

Jamhuriyar Nijar za ta rika shigo da man fetur Kasar Najeriya

Jamhuriyar Nijar za ta taimakawa Kamfanin Man Kasar da ke Kaduna

Najeriya za ta fara sayan man fetur daga Jamhuriyar Nijar
NNPC GMD Baru

Kasar Najeriya da Kasar Jamhuriyar Nijar sun shiga wata yarjejeniyar da za ta bunkasa harkar man fetur a Kasashen biyu masu makwabtaka. Wannan yarjejeniya za ta sa Jamhuriyar Nijar ta rika shigo da man fetur Kasar Najeriya.

Jamhuriyar Nijar za ta rika shigo da man fetur har Kamfanin Man Kasar da ke Garin Kaduna. Da alamu dai wannan ba zai rasa nasaba da matsalar da ake samu a Yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur a Kasar ba. Hakan ta sa man fetur din da Najeriya ta ke hakowa ya ragu kwarai da gaske.

KU KARANTA: CAN ta kai kuka wajen Shugaba Buhari

Tsagerun Neja-Delta suna ta ta’adi suna fasa butatan man Kasar, Najeriya da kan hako fiye da ganga Miliyan biyu a rana ta buge da hako Kasa da ganga Miliyan biyu. Vanguard tace Shugaban Kamfanin mai na NNPC na Kasar, Maikanti Baru ya bayyana wannan yarjejeniya bayan tattaunawa da Ministan mai na Jamhuriyar Nijar.

Haka kuma Najeriya za ta hada kai da Jamhuriyar Nijar wajen ganin an hako mai a Yankin Chad da Bangaren Benue na Arewacin Kasar Najeriya. Haka kuma za a ga yiwuwar kawo mai Garin Kaduna daga Jamhuriyar Nijar Inji Ministan main a Jamhuriyar Nijar, Faoumakoye Gado.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel