Hukumar EFCC ta saki Reuben Abati

Hukumar EFCC ta saki Reuben Abati

Hukumar EFCC ta saki Mai magana da bakin tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan

Dr. Reuben Abati ya tabbatar da cewa yanzu haka yana Abuja, bayan an sake shi

Ana zargin Reuben Abati ya karbi Miliyoyin kudi daga hannun Sambo Dasuki

Hukumar EFCC ta saki Reuben Abati
Tsohon kakakin shugaban kasa, Reuben Abati

Hukumar EFCC ta saki  mai magana da bakin Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Goodluck, watau Dr. Reuben Abati bayan ya sha tsari na kwana da kwanaki. Reuben Abati ya tabbatar da bakin sa cewa yanzu haka Hukumar EFCC ta sake shi a yau da safen nan.

Reuben Abati, mai ba tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan shawara game da harkokin sada labarai a wancan lokaci, ya bayyanawa Jaridar Premium Times cewa yanzu haka yau da safen nan, yana cikin Abuja, bayan Hukumar EFCC ta sake sa.

KU KARANTA: Ibrahim Magu yace ana masa makarkashiya

Ana zargin Reuben Abati ya karbi kudin makamai daga hannun mai ba tsohon Shugaban Kasa shawara kan tsaro, Sambo Dasuki. Don haka Hukumar ta kama Reuben Abati, inda tayi masa wasu tambayoyi. Ana cewa Reuben Abati ya karbi Miliyan 50 daga cikin kudin sayen makaman, wanda yace kyautar bikin kirismeti ne aka ba shi.

Reuben Abati yayi alkawarin maido wasu daga cikin kudin, sai daga baya kuma aka rahoto cewa, Reuben Abati ya bayyana cewa ba sa da kudin da zai bada. A jiya ma dai an saki wani Tsohon Minista lokacin Shugaba Jonathan, Musliu Obanikoro. Jaridar Punch tace ana binciken fiye da Ministoci 20 na Shugaba Jonathan da laifin cin kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel