Najeriya na shirin ciwo wani bashin

Najeriya na shirin ciwo wani bashin

- Bankin raya Afrika ya amince ya ba Najeriya rancen kudi dala miliyan 600 domin taimakawa shugaba Muhammadu Buhari magance matsalolin tattalin arziki da kasar ke fuskanta.

- Bankin na AFDB ya ce wannan mataki na farko ne daga cikin adadin kudi dala biliyan daya da Najeriya ke neman rance domin cike gibin kasafin kudinta na bana.

Najeriya na shirin ciwo wani bashin
President Buhari receives Dr Akinwunmi Adesina, the president of the African Development Bank, at the State House on September 26, 2016. Photo: Femi Adesina

Wannan na zuwa a yayin da Majalisar dattijai ta yi watsi da bukatar Buhari na ciyo bashin kudi dala biliyan 30 daga waje domin gudanar da ayyukan gwamnatin shi a cikin shekaru uku.

‘Yan Majalisar sun yi watsi da bukatar ne saboda rashin gamsassun bayanai akan dalilin cin bashin.

Kodayake shugaban ya ce zai sake aikawa da bukatar zuwa Majalisa domin sake diba bukatar ciyo bashin.

A farkon satin nan ne dai A Najeriya, babbar jam`iyyar adawar kasar wato PDP da wasu kungiyoyi sun ce ba sa goyon bayan shirin gwamnatin kasar na karbar rancen dala biliyon 30.

Gwamnatin dai na son karbo rance ne don cike gibin kasafin kudin kasar na shekara uku tare da aiwatar da wasu ayyukan inganta rayuwar jama`a.

Sai dai jam`iyyar adawa ta PDP ta ce kamata ya yi shugaba Buhari ya yi amfani da kudaden da gwamnatinsa ke ikirarin ta kwato daga hannun wasu da aka samu laifin sama da fadi da kudaden gwamnati wajen cike gibin kasafin kudin.

Sai dai jam`iyyar APC mai mulki ta ce PDP ta fi kowa sanin wadanda suka wawure kudaden kasar kuma ya kamata ta taimaka wajen kwato kudaden.

A ranar Talata ne majalisar dattawan kasar ta yi watsi da bukatar shugaban Buharin ta karbar rancen dala biliyon 30 daga waje don cike gibin kasafin kudin kasar na shekaru uku masu zuwa saboda ba a yi musu bayani a kan sharudan da ke tattare da bashin ba.

Sai dai mai taimaka wa shugaban kasar a kan harkokin majalisar wakilai, Hon Kawu Sumaila ya ce nan bada jima wa ba ne shugaban kasar zai sake gabatar da cikakken bayani ga Majalisar.

Shirin rancen dai ya hada da sayar da takardun bashi na kudin Euro da kuma shirin tallafawa kasafin kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel