An saki mutanen da ake zargi da kashe wata mata a Kano

An saki mutanen da ake zargi da kashe wata mata a Kano

- Wata kotu a Kano ta saki dukkanin mutane 5 da ake zargi sun kashe wata 'Yar kabilar Igbo Bridget Agbahime da aka zarga da yin batanci ga addini musulunci a Kofar Wambai

- A ranar 2 ga watan Yuni ne aka kashe Agbahime kan zargin yin batanci ga addinin Islama

An saki mutanen da ake zargi da kashe wata mata a Kano

Kotun Kano kuma ta saki dukkanin mutane 5 da aka zarga sun kashe mutumin dan kabilar Igbo daga Jihar Imo.

Lauyan da ke kare mutanen da ake zargi Malam Gambo ya tabbatarwa da majiyar mu cewa kotu ba ta same su da laifi ba.

Wasu rahotanni sun ce kotun ta wanke mutanen 5 ne kamar yadda alkalin alkalan jihar ya bukata.

A wani labarin makamancin wannan kuma Dubban Musulmi ne suke yin zanga-zanga a Indonesia, inda suke kira a hukunta gwamnan birnin Jakarta saboda ya yi ridda.

Basuki Tjahja Purnama, wanda Kirista ne, shi ne dan kabilar China na farko da ya zama gwamna a kasar da mafi yawan mutanenta Muslmi ne.

Masu zanga-zangar sun taru a Masallacin Istiqlal kuma daga nan suka nufi fadar shugaban kasar.

'Yan sanda sun daura damara domin tunkarar yiwuwar barkewar rikicin addini.

A shekarar 1998, an yi zanga-zangar kin jinin 'yan China lamarin da ya kai ga kona kantuna da da gidaje da kuma sace kayayyakin 'yan China.

'Yan kabilar China su ne kusan kashi daya cikin dari na al'umar Indonesia kimanin 250m.

Mr Purnama, wanda aka fi sani da "Ahok" na shirin sake tsayawa takara a watan Fabrairu na shekarar 2017.

Sai dai wasu Musulmi sun ce bai kamata ya tsaya ba, suna masu cewa bai kamata wanda ba Musulmi ba ya jagoranci Musulmi.

https://youtu.be/KhUBU4G1n0U

Asali: Legit.ng

Online view pixel