Man United sun sha kashi

Man United sun sha kashi

- Fernebahce ta doke Manchester United 2-1 a karawar da suka yi ta biyu ta kofin Zakarun Turai na Europa wasan mako na hudu na rukunin farko.

- Kungiyar ta birnin Istanbul ta fara daga ragar bakin nata ne a cikin minti biyu kacal da shiga fili ta hannun dan wasanta Sow, wanda ya shammaci 'yan United din ya yi kwance-kwance da baya ya sheka musu ita a raga.

Man United sun sha kashi
Manchester United

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma a minti na 59 J. Lens ya kara kwallo ta biyu a ragar Manchester United.

Wayne Rooney ya rama wa Man United din kwallo daya ana dab da tashi daga wasan a minti na 89.

Kwallon ta Rooney ita ce ta 38 da ya ci a gasar Zakarun Turai, wadda ta sa ya kamo Ruud van Nistelrooy a matsayin wanda ya fi ci wa United kwallo a gasar Zakarun Turai.

Sakamakon ya sa United ta zama ta uku a rukunin na farko (Group A), da maki daya a bayan Feyenoord da Fenerbahce.

Kuma hakan ya jefa ta cikin hadarin kasa zuwa mataki na gaba na sili-daya-kwale, na gasar ta kofin Europa.

Wasa biyu ya rage wa kungiyar ta Premier, inda za ta kara a Old Trafford da Feyenoord ta Holland, sannan kuma ta je Ukraine ta hadu da Zorya Luhansk.

A karawarsu ta farko mako biyu da ya gabata Manchester United ta ci Fernebahce 4-1 a Old Trafford.

A daya karawar da ka yi ta rukunin na daya Zorya Luhansk da Feyenoord sun yi canjaras 1-1.

A wani labari makamancin wannan kuma Kocin Arsenal, Arsene Wenger, ya ce Fifa, ba ta yi daidai ba da ta hana 'yan wasa sanya kyallaye masu alamar tunawa da sojin Burtaniya da na Commonwealth da suka mutu a yakin duniya na daya da sauran rikice-rikice, a wasan neman shiga gasar kofin duniya da Ingila za ta yi da Scotland.

Kocin na Arsenal ya ce, bai kamata Fifa ta shiga wannan lamari ba, yana mai karin bayani da cewa, wani lokaci idan kana son ka nuna cewa daidai kake a kan akidarka ta siyasa, sai ka dan saba wa al'ada.

Kocin ya ce, ina ganin wannan na daga al'adar Ingila da nake kauna. Suna mutunta al'ada, kuma suna martaba mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu ga kasar.

Ita dai hukumar ta haramta sanya sakonnin siyasa ko addini ko wata talla a jikin rigunan 'yan wasa.

Ita dai wannan alama ana sanya ta ne a makonnin kusa da kuma ranar 11 ga watan Nuwamba, domin tunawa da sojin na Burtaniya da na kungiyar kasashen renon Ingila da suka mutu a yakin duniyar na daya da sauran yake-yake da suka biyo baya.

Babbar Sakatariyar Fifa, Fatma Samba Diouf Samoura za ta gana da ranar Alhamis din nan da hukumomin kwallon kafa da ke Burtaniya a filin wasa na Wembley, kuma mai yuwuwa su tattauna a bayan fage kan batun in ji wakilin BBC.

Samoura ta sheda wa BBC cewa, kowane irin hukunci zai iya biyo baya, idan aka saba wannan umarni na hukumar ta kwallon kafa ta duniya.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Ingila, Martin Glenn, ya gaya wa BBC cewa, 'yan wasan bangarorin biyu za su yi watsi da wanna umarni na Fifa, su sanya wannan jar alama, a matsayin al'adarsu.

Ita ma hukumar kwallon kafa ta Scotland ta ce a shirye take ta kalubalanci duk wani hukunci da Fifa za ta yi wa 'yan wasanta kan daura kyalle a hannuwansu, wato wannan alama.

A ranar Juma'a ta sama ne 11 ga watan Nuwamba kungiyoyin na Ingila da Scotland za su kara a wasan neman tikitin zuwa gasar cin kofin duniya na 2018, a filin wasa na Wembley.

Fifa dai ta bar 'yan wasan Ingila da na Scotland din sun sanya wannan alama da yanzu ake wannan ja-in-ja a kanta, a kan bakin kyalle, suka daura a hannuwansu, a lokacin wasan kasa da kasa a watan Nuwamba na 2011.

https://youtu.be/KhUBU4G1n0U

Asali: Legit.ng

Online view pixel