An karrama manjo Hamza Al-Mustapha a kasar waje

An karrama manjo Hamza Al-Mustapha a kasar waje

An karrama tsohon mai gadin tsohon shugaban kasa janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha a garin kwatano, tarayyar kasar Benin.

An karrama manjo Hamza Al-Mustapha a kasar waje

Jami’an Esep-Le Berger ce ta karrama shi da lambar girmaamwar Dakta a fannin yima al’umma hidima (Doctor of Humanities (Honorary Causa)) a taron bikin yaye daliban ta.

Sai dai ba Al-Mustapha kadai aka karrama ba, har da wasu yan Najeriya shahararru su biyar da suka hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero, Alhaji Balarabe Musa, Segun Akinlolu (Beautiful Nubia), shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Bauchi kwamared Muhammed Gital, da Alhaji Jubril Muhammed.

KU KARANTA: Gadar data hada jihohin Oyo da Kwara ta sake karyewa

Kimanin dalibai 700 aka yaye daga jami’ar, da dama daga cikinsu sun fito ne daga kasashen yammacin Afrika, An gudanar da taron yaye su ne a dakin taro na Palais De Congress dake garin Kwatano, taron yayi armashi inda kusan baki 2000 ne suka samu halartan bikin.

Shugaba kuma wanda ya assasa jami’an Farfesa Germain Ganlonon yace jami’ar ta zabo Manjo Al-Mustapha ne sakamakon ayyukan jin kai da yake yi ma talaka. Shima Al-Mustapha yace wannan lambar yabo daya samu zata kara masa kaimi waken cigaba da ayyukan alheri dayake yi ma al’umma, duk abinda mutum yayi, walau alheri ko sharri, jama’a na kallo, kuma zasu saka maka iya bainda kayi.

Idan mai karatu bai manta ba, an kama Manjo Hamza Al-Mustapha ne a 1998 da kan zarginsa da ake yi da hannu cikin kashe Kudirat Abiola, matar Moshood Abiola. Bayan kwashe shekaru a gidan yari ne kotun daukaka kara ta wanke shi daga laifukan a ranar 12 ga watan Yulio shekara ta 2013.

&index=24&list=PL6sEiOi0w1ZCJ2pYczvQeEWNY5u811xJt

Asali: Legit.ng

Online view pixel