Tsohuwar Matar Cif Obasanjo za ta kafa sabuwar Jam’iyya

Tsohuwar Matar Cif Obasanjo za ta kafa sabuwar Jam’iyya

- Tsohuwar matar tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo za ta kafa sabuwar Jam’iyyar siyasa

-  Misis Taiwo za ta bude sabuwar Jam’iya mai suna ABC

Wata tsohuwar matar Cif Obasanjo za ta kafa Jam’iyya mai suna ABC, watau Abundant Blessing Congress

Tsohuwar Matar Cif Obasanjo za ta kafa sabuwar Jam’iyya
Taiwo Obasanjo

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Wata daga cikin Tsohuwar matar Tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo za ta kafa sabuwar Jam’iayyar siyasa. Misis Taiwo, tana daya cikin wadanda suka taba auren Shugaba Obasanjo, za ta bude wata sabuwar Jam’iyya mai suna ABC-watau Jam’iyyar Abundant Blessing Congress.

Tsohuwar Matar Shugaban Kasa tace ba daidai bane a cigaba da ganin laifin Shugaba Buhari wajen tabarbarewar abubuwa a Kasar. Tsohuwar Matar Cif Obasanjo tace Shugaba Buhari yana kokarin shawo kan matsalolin Kasar ta Najeriya.

KU KARANTA: Shugaban kwastam ya maido kudi

Misis Taiwo ta bayyanawa Jaridar The Sun cewa Ubangiji ne ya turo ta ta kafa wannan Jam’iyya a Kasar. Madam Taiwo tace Ubangiji ne ya turo ta, ya kuma sa ta wannan aiki, tace Jam’iyyar su za ta ba kowane mara karfi karfi domin ganin Kasar Najeriya ta ci gaba.

Taiwo take cewa za su taimakwa wajen ganin Najeriya ta ci gaba. Tsohuwar Matar Shugaban Kasa tace sam ba daidai bane a rika ganin laifin Shugaba Buari wajen yadda abubuwa suka cabe a Kasar, tace shakka babu, Shugaba Buhari ya zo gyara ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel