Zazzafar muhawara game da kudurin Buhari

Zazzafar muhawara game da kudurin Buhari

- A Najeriya, babbar jam`iyyar adawar kasar wato PDP da wasu kungiyoyi sun ce ba sa goyon bayan shirin gwamnatin kasar na karbar rancen dala biliyon 30

- Gwamnatin dai na son karbo rance ne don cike gibin kasafin kudin kasar na shekara uku tare da aiwatar da wasu ayyukan inganta rayuwar jama'a

Zazzafar muhawara game da kudurin Buhari
President Buhari has promised to focus more on agriculture

Sai dai jam`iyyar adawa ta PDP ta ce kamata ya yi shugaba Buhari ya yi amfani da kudaden da gwamnatinsa ke ikirarin ta kwato daga hannun wasu da aka samu laifin sama da fadi da kudaden gwamnati wajen cike gibin kasafin kudin.

Sai dai jam`iyyar APC mai mulki ta ce PDP ta fi kowa sanin wadanda suka wawure kudaden kasar kuma ya kamata ta taimaka wajen kwato kudaden.

A ranar Talata ne majalisar dattawan kasar ta yi watsi da bukatar shugaban Buharin ta karbar rancen dala biliyon 30 daga waje don cike gibin kasafin kudin kasar na shekaru uku masu zuwa saboda ba a yi musu bayani a kan sharudan da ke tattare da bashin ba.

Sai dai mai taimaka wa shugaban kasar a kan harkokin majalisar wakilai, Hon Kawu Sumaila ya ce nan bada jima wa ba ne shugaban kasar zai sake gabatar da cikakken bayani ga Majalisar.

Shirin rancen dai ya hada da sayar da takardun bashi na kudin Euro da kuma shirin tallafawa kasafin kudi.

https://youtu.be/KhUBU4G1n0U

Asali: Legit.ng

Online view pixel