El-Rufai ya sasanta rikicin masallacin Sultan Bello

El-Rufai ya sasanta rikicin masallacin Sultan Bello

- Bangarorin da ke rikicin shugabanci a kan masallacin Sultan Bello da ke Kaduna sun sasanta bayan da gwamnatin jihar ta shiga tsakani

- Matakin da gwamnan jihar ya dauka shi ne na cewa a bar mataimakin limamin ya ci gaba da limanci a matsayin wucin-gadi kafin a nada limami na din-din

El-Rufai ya sasanta rikicin masallacin Sultan Bello
Vans were spotted in front of the mosque this Friday, October 28

Kwamitin masallacin bisa hadin guiwa da Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, da kungiyar Jama'atu Nasril Islam da bangaren Dakta Ahmad Gumi da sauran masu ruwa da tsaki su aka dora wa alhakin nada sabon limamin.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Samuel Aruwan, ya fitar, ya ce, an kawo karshen rikicin ne bayan wani zama da bangarorin suka yi a gidan gwamnati, wanda gwamnan jihar Nasir Ahmad El-Rufai ya shirya.

Sanarwara ta ce bayan da gwamnan ya ji bayanin dukkanin bangarorin da ke rikicin, ya ce gwamnati ta shiga tsakani ne saboda tsaro kawai, amma ba domin wani abu ba.

Sannan ya yi gargadin cewa gwamnati ba za ta lamunta da duk wani mataki na karya doka ba da sunan addini, da kuma barin mutane suna nema wa kansu mafita ba kan wata matsala.

A wani labarin kuma An fara bikin cika shekaru goma da Sarkin Musulmi Mai Martaba Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III ya dare kan karagar mulki a Sokoto.

Jiya aka fara bukuwan a birnin Sokoto tare da yin addu'o'i na samun zaman lafiya da cigaban kasar Najeriya tare kuma da neman sauki daga cikin mawuyacin halin da 'yan kasar ke ciki.

Bayan kammala addu'o'in a karkashin sarkin Kano Muhammad Sanusi II jawaban da suka biyo bayan addu'o'in tamkar martani ne ga wasu dake kushin taron binkin cewa ya zo daidai lokacin da 'yan Najeriya ke fama da kuncin rayuwa da kuma mutuwar dimbin mutane a Sokoto sanadiyar barkewar cutar zazzabin cizon sauro.

Sultan Sa'ad Abubakar III yace bikin na yiwa Allah godiya ne akan matsayin da Allah ya dorashi. Yace taro ne na godiya ba na nishadi ba saboda a matsayinsu na musulmai sun kara haduwa, sun kara hada kai domin godewa Allah.

https://youtu.be/KhUBU4G1n0U

Asali: Legit.ng

Online view pixel