Karanta labaran da suka girgiza Najeriya a jiya

Karanta labaran da suka girgiza Najeriya a jiya

Jaridar Legit.ng ta tattaro muhimman labaran da suka girgiza kasar a ranan talata,1 ga watan Nuwamba

1. Gwamna Amosun ya kori shugabannnin NLC, TUC da NUT

Karanta labaran da suka girgiza Najeriya a jiya
Governor Ibikunle Amosun

Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun ya tabbatar da Koran shugabannin kungiyoyin kwadago ta NUC, NUT a jihar ta Ogun. Wannan kora ya faru ne bayan ma’aikatan jihar Ogun suka tafi yajin aiki kwana 11.

2. EFCC na binciken Sabon ango, sirikin Shugaba Buhari

Karanta labaran da suka girgiza Najeriya a jiya
Malam Gimba Yau Kumo

Tsohon dirakta manajan bankin kananan gidaje na tarayya, Malam Gimba Yau Kumo, kuma sabon ango sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari, yana karkashin binciken hukumar EFCC.

3. Dan sanda ya daba ma kwandasto wuka yar lahira akan N100

Karanta labaran da suka girgiza Najeriya a jiya

Wata tashin hankali da ta faru a ranan asabar,29 ga watan oktoba , a Ojodu Berger bus stop,jihar Legas, inda wani dan sanda ya Burma ma wani dan gareyi kaifi har lahira.

4. Shugaba Buhari ya ganawa a shugabannin yankin Neja- Delta

Karanta labaran da suka girgiza Najeriya a jiya

Shugaba Muhammadu Buhari ya kasance yana baiwa yan yankin Neja Delta daman ganawa da shi. Ana sa ran ganawar zata magance rigingimun da ke faruwa a yankin mai arzikin man fetur wanda ya durkusar da tattalin arzikin kasar.

5. An gano wasu yan sanda 2 suna dambatawa a fili

Karanta labaran da suka girgiza Najeriya a jiya

Game da cewar hotunan da suka bayyana a kafafen sada zumunta da ra’ayi ta yanar gizo, an gan yan sandan sun baiwa hanmata iska suna dambe kuma mutanr usn gaza raba su duk da cewan abokan aikinsu sunyi kkarin raba su.

6. Biafra: Minista ya shawarci masu fafutuka sunyi aiki da tsarin doka

Karanta labaran da suka girgiza Najeriya a jiya

Ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama ya bayar da shawara ga duk masu fafutukar neman kasar Biafra. Onyeama yayi magana a karshen mako a Jihar Enugu inda yace duk gungunan masu neman 'yancin Biafra dole ne subi kai'dojin kundin tsarin mulki da kuma hanyoyin diplomasiyya wajen neman bukatarsu.

7. Kotun daukaka kara ta ki yanke hukunci akan zancen PDP

Karanta labaran da suka girgiza Najeriya a jiya

Kotun daukaka kara ta ki yanke hukunci akan al’amarin da ya shafi bangarorin jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP guda biyu.

8. Majalisar dattawa ta ki amincewa da bukatar Buhari ya amso bashin N12 triliyan

Karanta labaran da suka girgiza Najeriya a jiya

Majalisar dattawan Najeriya tayi watsi da yunkurin shugaba Buhari na amso bashin N12 triliyan domin gudanar da wasu ayyuka a fadin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel