Hukumar EFCC sun tsare kanin tsohon gwamna

Hukumar EFCC sun tsare kanin tsohon gwamna

- Hukumar hana cin hanci da rashawa EFCC sun kama kuma sun tsare kanin tsohon gwamnan jahar Akwa Ibom, Ibanga Akpabio                                             

- Hukumar EFCC ta kama Akpabio da laifin satar kudin gwamnati                    

- Ibanga Akpabio shine mataimakin shugaban jam'iyar PDP na jahar Akwa Ibom

Wani rihoto da sahara reporters suka dauki alhakin ruwaito wa sunce hukumar EFCC ta kama kanin tsohon gwamnan jahar Akwa Ibom Ibanga Akpabio .

Hukumar EFCC sun tsare kanin tsohon gwamna

Kamar yadda rohoton ya bayyana , Ibanga Akpabio wanda a halin yanzu shine mataimakin shugaban jam'iyar PDP na jahar Akwa Ibom, hukumar ta EFCC ta kama shi da laifin sata da almundahana.

Ibanga kani ne ga Godwill Akpabio wanda a halin yanzu dan majalisar dattijai ne kasar nan.

Kamar yadda muka ji daga EFCC cewa Ibanga yana tsare a reshen hukumar EFCC dake fatakot saboda damfarar wani dan majalisar wakilai da yayi Robinson Uwak.

Haka kuma ana nan ana tuhumar shi kan sata da almun dahana da kudin kasa kamar yadda jami'an hukumar suka bayyana.

Tsohon gwamnan jahar Akwa Ibom an bincike a hukumar EFCC  na wasu awanni kan debe kudin jahar na biliyoyin nairori, wanda ya fito ya musanta haka. Har yanzu ana kan binciken.

Sai dai ba dadewa sahara reporters sun bayyana muryar telefon din da suka dauka na Ibanga Akpabio inda ya ke cika bakin abunda ya hada su da EFCC da shugaban hukumar Ibrahim Magu.

Sai dai kuma Legit.ng ba zasu iya tsayawa su gano tabbacin muryar da zaku ji a kasa.

https://m.youtube.com/watch?v=Gdnq7olD-GA

Asali: Legit.ng

Online view pixel