Messi yayi fada bayan sun sha kayi a hannun Man City

Messi yayi fada bayan sun sha kayi a hannun Man City

Fitaccen dan kwallon kungiyar Barcelona Lionel Messi ya shiga bakin duniya bayan yayi rigima da wani dan wasan Man City da ba’a ambaci sunansa ba yayin da suke fita daga fili, inji jaridar The Mirror.

Messi yayi fada bayan sun sha kayi a hannun Man City

Kungiyar Manchester City ta lallasa takwarar ta Barcelona 3-1 a filin wasa na Etihad. Messi ne ya fara zura kwallo a zaren Man City. Mintuna kadan Ilkay Gundogan ya farke ta, ida shima ya jefa kwallo a zaren Barcelona, daga nan sai Kevin De Bruyne ya kara ci ma Man City kwallo.

Gab da tashi wasa ne Ilkay Gundogan ya kara zura kwallo wanda hakan ya baiwa Man City nasarar da za’a iya kirar ta ramuwar gayya akan Barcelona.

KU KARANTA: Uwa, yayanta da makwabta sun mutu bayan cin tuwon Amala

Wani rahoton da ba’a tabbatar ba ya bayyana cewa Messi yayi cacar baki da wani dan wasan Man City yayin da suke kan hanyar fita daga filin wasa, ana zargin dan wasan City ne ya fara zagin Messi, inda shima Messi ya rama yace masa ‘Gabo’

Jaridar The Mirror ta ruwaito Messi ya tafi hard akin canza kaya na yan wasa don neman wannan dan wasan da ya tsokane shi, an jiyo shi yana cewa a fusace “ka dawo mana idan ba tsoro ba, ya kake boyewa” daga nan ne abokinsa Sergio Aguero ya lallashe shi.

&index=39&list=PL6sEiOi0w1ZCj2ZtMCJrZEAX8ccphZOIf

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel