Janar Buratai na sace alawus din ma'aikata - Inji sojojin Najeriya

Janar Buratai na sace alawus din ma'aikata - Inji sojojin Najeriya

Daga Edita, zaka bauta ma kasarka, ka sanya ranka cikin hadari, amma kuma kasarka taci amanarka, ta kuma manta da kai.

Wannan shine dai-dai abinda ya faru ga Ebuka Emeka da sauran ma'aikatan sojojin Najeriya wadanda ke zargin Janar Tukur Yusuf Buratai da sauran manyan jami'an soja da batar da kudaden da ya kamata aba sojoji.

Mista Emeka ya tuntubi Legit.ng domin taimako kan yadda za'a yi maganin abin da kuma samun isa ga Buratai, yana mai cewa za'a iya shiga rudani idan aka yi watsi da bukatunsu. Abin damuwa ne cewa babban hafsan hafsoshin sojojin Najeria mai ci Lutenan Janar Tukur Yusuf Buratai na kwace mana alawus dinmu.

KU KARANTA: Labari mai dadi: Shugaba Buhari zai kara albashin ma’aikata

Yadda suke zaluntar mu: Sojoji sun koka kan yadda wasu janar-janar na soja tare da hadin kan mista Buratai suke daukar alawus dinsu domin amfanin kansu a kai- a kai. Yace wannan dabi'ar na karya laggwan sojojin dake aiki a kasashe irin su Liberiya, Mali da Sudan. Sojojin na kuma koken cewa rabin alawus dinsu kadai aka biya su duk da yake sun gama aikinsu a kasashen waje. Amma abin ban takaicin shine shugaban sojojin bai damu da lafiyar sojojinsa ba, sai abinda zai sa aljihunsa.

Sojojin suna tambaya: Yaya zasu je kasashen waje aiki, su dawo gida su iske shugabannin su sun  kwashe kudaden su?

Asali: Legit.ng

Online view pixel