Sojoji sun ceto kananan yara 19 daga hannun Boko Haram

Sojoji sun ceto kananan yara 19 daga hannun Boko Haram

Rundunar mayakan Sojan kasa ta habbaka kokarinta na kakkabe yayan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram daga kafatanin kasar nan, yayin da ta kashe mutane 6 a wani hari da ta kai ma kungiyar.

Kaakakin rundunar Kanal Usman Kukasheka ya sanar da haka inda yake cewa mayakan rundunar sun kai hari a kauyukan Momo da Tushe dake kusa da garin Marten a jihar Barno. Yace yan mata 18 da yara 19 suka ceto, yayin da suka kashe yan kungiyar Boko Haram 6.

Sojoji sun ceto kananan yara 19 daga hannun Boko Haram
Mutanen da aka ceto

Kukasheka yace “rundunar mayaka ta 8 sun fara wani aiki na musamman ai suna ‘Operaition HARDKNOCK’ don karar da yayan kungiyar Boko Haram da suka boye a sassan arewacin jihar Barno, kan iyakar Najeriya da Chadi.

Yayin gudanar da aikin, rundunar ta kashe mayakan Boko Haram su 6, inda sauran suka tsere da harbin harsashi, sun gudu sun bar Babura 22, tutarsu da sauran kayayyaki. A wani labarin kuma mutane 9 ne suka rasa rayukansu da safiyar ranar Talata 1 ga watan Nuwamba bayan bom ya tashi a cikin wata mota kirar A-kori-kura a jihar Barno.

KU KARANTA: Keke NAPEP mai amfani da hasken rana (Hotuna)

Rahotanni sun bayyana cewa motar na dauke da kayan fashewa ne yayin da suka tashi, inda suka yi sanadiyyar kashe dukkanin fasinjojin motar su 9.

An bayyana cewa motar ta fito daga dajin kan titin Maiduguri zuwa Gubio dauke da fasinjoji su 9, sai dai ta kama da wuta bayan ta hau kan titin kwaltar daya nufi garin Gubio, kimanin kilomita 80 daga garin Maiduguri.

&list=PL6sEiOi0w1ZCRr8pA_MK35Fz3HHqWzhFQ&index=25

Asali: Legit.ng

Online view pixel