Dan sanda ya daba ma kwandasto wuka yar lahira akan N100

Dan sanda ya daba ma kwandasto wuka yar lahira akan N100

- Wani dan sanda ya daba ma wani dan gareji wuka a garejin mota da ke zuwa daga jihar Oyo

- An kaishi asibitin gaggawa da wuri amma aka tabbatar da cewa a kwanta dama

Dan sanda ya daba ma kwandasto wuka yar lahira akan N100

Wata tashin hankali da ta faru a ranan asabar,29 ga watan oktoba , a Ojodu Berger bus stop,jihar Legas, inda wani dan sanda ya Burma ma wani dan gareji kaifi har lahira.

Dan sandan na cikin wata mota ne daga tafiya daga jihar Oyo zuwa Legas ,inda ya kashe dan garejin.

KU KARANTA:Doka! Duk wanda aka kama da laifin satar mutane a jihar Kano zai fuskanci wannan mummunan hukuncin

Sunan marigayin Ahmed wanda ke shirin aure a watan disamba mai zuwa. Jaridar Punch ta bada rahoton cewa Ahmed ya tare motan ne ya nemi a bashi N100 amma direban yaki,  da aka fara cecekuce tsakanin direban da Ahmed, said an sandan ya fito daga cikin motar.

“Kawai said an sanda ya fito da wata wuka mai kaifi daga aljihunsa ya ya Burma masa a ciki. Ai ya fara magagin mutuwa. Idan shaida yace.

An kai Ahmed asibiti da wuri a jihar Legas amma ya riga ya cika.

Wani abokin Ahmad mai suna Agberoko, yace jami’an yan sandan Rapid Response Squad (RRS) sun harba barkonon tsohuwa saboda ceton dan sandan da yayi kisan kai.

“Jami’an Rapid Response Squad (RRS) suka fara harbi sama kuma suka hara barkonon tsohuwa . an dawo da gawar Ahmed tasha ,kuma abokansa na cikin fushi wanda yasa sukayi wuji-wuji da motan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel