Malaman makaranta a Taraba na cikin mawuyacin hali

Malaman makaranta a Taraba na cikin mawuyacin hali

- Kungiyar Malaman firamari ta kasa reshen karamar hukumar Donga dake jihar Taraba ta Kai kokenta na rashin biyan wasu mambobinta albashin wata takwas ta hanyar daukar azumi na kwanaki uku

- Wannan matakin na zuwa biyo bayan tankade da rairayar da gwamnatin ta kaddamar don gano malaman bogi wanda ya yi sanadin rashin biyan mutane su dari hudu da casa'in da bakwai Inji daya daga cikin wadanda abin ya shafa Malam

Malaman makaranta a Taraba na cikin mawuyacin hali
Governor Darius Ishaku of Taraba state

Mahi Umar wanda ya ce duk da kin biyansu hakkokinsu suna zuwa aiki.

Shugaban kungiyar malaman na kasa reshen karamar hukumar Donga Komred Danladi Ibrahim ya shaidawa majiyar mu cewa ba su da zabi illa su kai kokensu gaban Allah ganin kwalliya ba ta mai da kudin sabulu ba duk da daukar dukkan matakan da suka halartar.

Shi ma shugaban kungiyar reshen jihar Taraba Komred Aliyu Tafida ya yace sun bukaci gwamnatin ta sake tantance wadanda aka tsaida albashinsu amma zahiri har yanzu bata basu wata amsa takamaimiya ba.

Da yake kare matsayin gwamnatin jihar Taraba, shugaban hukumar kula da makarantu firamare Mal. Yakubu Saleh yace tankaden ya bankado malaman bogi dubu daya da dari bakwai kuma gwamnati na fatar da zarar an kammala tankade da rairayar zata maido da kudade da za a karkata wajen yi wa jama'a hidima.

A wani labarin mai kama da wannan kuma Bincike ya nuna cewa hukumar EFCC na tuhumar sabon sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wato Ya'u Gimba Kumo kan wasu naira bilyan 3 da suka salwanta a lokacin da yake manajan darakta na bankin FMBN, kamar yadda majiyarmu ta Sahara Reporters ta rawaito

Shi dai Ya'u Kumo shine aka daura aurensa da 'yar shugaba Buhari mai suna Fatima a makon da ya gabata a garin Daura.

https://youtu.be/nT0m4FpgP-w

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel