EFCC na binciken Sabon ango, sirikin Shugaba Buhari

EFCC na binciken Sabon ango, sirikin Shugaba Buhari

- Hukumar EFCC na binciken sirikin shugaba Buhari

- Gimba Ya’u Kumo ya kasance Dirakta Mnanjan bankin ne daga Disamban 2010 zuwa Agustan 2014

EFCC na binciken Sabon ango, sirikin Shugaba Buhari
Malam Gimba Yau Kumo

Tsohon dirakta manajan bankin kananan gidaje na tarayya, Malam Gimba Yau Kumo, kuma sabon ango sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari, yana karkashin binciken hukumar EFCC.

Jaridar Sahara Reporters ta bada rahoton cewa a yanzu haka hukumar EFCC na gudanar da bincike akansa saboda wata Almundahana da ta faru a lokacin da yake manajan bankin FMBN.

KU KARANTA:Shugaba Buhari yaba da umurnin yin bincike akan zargin lalata da Yan gudun hijira

 “Sabon ango sirikin Buhari ,Yau Kumo yana karkashin bincike a EFCC akan almundahanan N3bn da yayi lokacin kulkinsa a FMBN.

Zaku tuna cewa, a makon da ya gabata, ‘yar shugaba Buhari ta biyu, Hajiya Fatima ta auri Yau Kumo a garin Daura ,Katsina.

Gimba Ya’u Kumo ya kasance Dirakta Mnanjan bankin ne daga Disamban 2010 zuwa Agustan 2014.

Asali: Legit.ng

Online view pixel