Kano ta tsira da Ganduje a matsayin gwamna- Tambuwal

Kano ta tsira da Ganduje a matsayin gwamna- Tambuwal

- Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa jihar Kano na cikin hannu mai kyau tunda ta samu Dr Abdullahi Ganduje a matsayin gwamna

- Tambuwal yace Ganduje yayi gwaninta ba wai ta hanyar ci gaba da ayyukan da ya gada kawai ba amma harma ga samar da sabbabin ayyuka duk da karancin kudaden shiga

Kano ta tsira da Ganduje a matsayin gwamna- Tambuwal
Gwamna Ganduje tare da Gwamna Tambuwal cikin raha

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa jihar Kano na tsare kuma cikin hannu mai kyau tunda ta samu Dr. Abdullahi Ganduje a matsyin gwamna.

Tambuwal wanda ya kimanta Ganduje bisa ga dunbin tarin kwarewarsa, ya kara da cewa, gwamnan yayi kokari ba wai ta hanyar ci gaba da aikin da ya gada ba harma da samar da sabbabin ayyuka duk da karancin kudin shiga.

KU KARANTA KUMA: An kama yan Najeriya uku suna sata a Dubai

Yayinda ya ci gaba da nanata cewa, Kano kamar jihar Sakkwato Allah ya albarkace su da yan siyasa balaggagu, masu hikima, da kuma kwazo, Tambuwal yace har yau jihar Kno da jihar Sakkwato suna biyan albashi lokacin da wasu jihohi ke rike da albashin ma’aikata.

Tambuwal yaba gwamna Ganduje tabbacin cewa manufarsa na kawo mambobin gwamnatinsa jihar Sakkwato domin titaya ra’ayi ne mai kyau, domin jihar Sakkwato ta kasance mafi zaman lafiya a Najeriya.

Da yake magana da farko, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduja, ya bayyana cewa suna birnin Shehu donmin wani ritaya kamar yadda jihar keda dunbin tarihi a shugabanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel