Majalisa za ta rushe akaun din hadaka na Kananan Hukumomi

Majalisa za ta rushe akaun din hadaka na Kananan Hukumomi

- Ana kokarin samawa Kananan Hukumomi ‘Yanci a Najeriya

- Majalisar dokoki za ta rushe akaun din hadaka na Jihohi da Kananan Hukumomi

Hakan zai taimakawa Kananan Hukumomin Kasar nan

Majalisa za ta rushe akaun din hadaka na Kananan Hukumomi

 

 

 

 

Majalisar dokokin kasar nan na shirin kawo tsarin da zai soke amfani da akau din hadaka tsakanin Jihohi da Kananan Hukumomin Kasar nan. Majalisar ta bayyana cewa wannan kudirin yana cikin sabon tsarin da ake shirin kawowa.

Shugaban Kwamitin Jihohi Kananan Hukumomi na Majalisar Dattawar, Sanata Abdullahi Abubakar ya bayyanawa manema labarai cewa ana shirin soke tsarin amfani da gamamen akau tsakanin Jihohi da Kananan Hukumomi a Kasar nan, Sanata Abdullahi yace wannan yana cikin garambawul din da ake kokarin zuwa da shi Majalisar.

KU KARANTA: 'Yar Najeriya ta kafa tarihi a wata Kasa

Majalisar Dattawa na shirin kawo garambawul a kundin tsarin mulkin Kasa wanda zai shafe akau din hadaka da kuma Hukumomin zabe na Jihohi. Wannan kudirin zai taimakawa Kananan Hukumomi a Kasar nan, wajen zaben Shugabannin su da kuma magance matsalolin da suka shafe su.

Sanata Abdullahi Abubakar yace hakan zai ba Kananan Hukumomi maganin matsalat tsaro da yanzu ya tabarbare. Kananan Hukumomi sun dai dade suna kukan cewa Jihohi na danne su a Kasar. Kwanakin baya sun gana da Shugaba Buhari inda yayi alkawarin taimaka masu wajen sama masu ‘Yancin su.

&list=PL5WFXwBsz6_9jqy5njKogV-vLjxIFd3LK

Asali: Legit.ng

Online view pixel