Dalibai ‘yan makaranta sun yi hadari a hanyar dawowa hutu

Dalibai ‘yan makaranta sun yi hadari a hanyar dawowa hutu

- Wasu dalibai 'yan makaranta FGGC Oyo sun yi hadari a mota wajen dawowa hutu gida yada zango

- Wata katuwar mota ta fada kan ‘yan makaranta inda ta kashe dalibai hudu

- Wasu daga cikin ‘yan makaranta sun mutu har lahira, wasu kuma sun jikkata

Dalibai ‘yan makaranta sun yi hadari a hanyar dawowa hutu

 

 

 

 

 

 

Wata katuwar mota ta fado kan yara dalibai ‘Yan makaranta, inda ta latse wasu daga cikin su har lahira. Wannan abin takaici ya faru ne a hanyar dawowa gidan ‘yan makaranta domin hutun yada zango. Wannan katuwar gingimari tana dauke ne da Garri, tayi sandiyar mutuwar dalibai har guda hudu.

Wannan mummunan abu ya auka ne da dalibai ‘yan makaranta Sakandare ta mata watau FGGC Oyo. An rasa dalibai hudu da kuma direba daya a wannan mummunan hadari. The Nations ta rahoto cewa, wannan hadari ya faru ne a Ranar Lahadi daidai karfe 3:30 na Yamma a kusa da wata kasuwa da ke Garin Sabo da ke kusa da Garin Oyo.

KU KARANTA: An haifi yaro da kafa hudu

Wata gingimari dauke da Garin rogo ta fada kan daliban ne inda ta kashe guda hudu nan take da kuma Direban motar. Daliban da suka rasa rayukan nasu su ne; John Olubukola, Giwa Taibat, Ladipo Mojisolo, Ibirogba Maryam; Daliban ‘Yan aji uku ne zuwa shida. Tuni dai aka bizne wadannan dalibai cikin kuka da jimami.

Sai dai guda biyar sun samu damar tsira da ran su, tuni dai ‘Yan Sanda sun kama direban wannan babbar mota.

&list=PL6sEiOi0w1ZDg4J68wF9HQxGPlWzlg-F5

Asali: Legit.ng

Online view pixel