Jikar Shagari zata auri sirikin Namadi Sambo

Jikar Shagari zata auri sirikin Namadi Sambo

Jikanyar tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari wanda ya karbi mulki a hannun janar Obasanjo, Nana zata shiga daga ciki.

Jikar Shagari zata auri sirikin Namadi Sambo

A watan Disambar bana ne ake sa ran gudanar da bikin auren Saleh Lukat da Nana Shagari wadanda suka dade soyayya da juna.

Idan ba’a manta ba, a kwanakin baya ne wata jikar Shehu Shagari Zara ta auri Faisal Umar Idris yaron tsohon minista Umar Idris.

Shahararren mai sana’ar dakan hoto George Okoro ne ya dauki hotunan Amarya da Angon, sa’anna ya bayyana ma Legit.ng cewar shi zai yi musu aikin hoto a yayin shagulgulan bikin.

Daga ganin ma’auratan kai kasan Nana kyakkyawace, shi ko Saleh yayi sa’ar mata yar babban gida, kuma gidan mutunci.

KU KARANTA: N10,000 nake siyan kawunan mutane, inji Boka

Jikar Shagari zata auri sirikin Namadi Sambo

Nana bata dade da kammala karatun harkar shari’ah ba a jami’a Leicester dake kasar Birtaniya, a yanzu haka tana makarantar kwarewa akan harkokin shari’a na Najeriya.

Shi kuwa Ango Saleh kani ne ga Amina Namadi Sambo, Uwargidar tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, kuma ya kasance dan kasuwa, shahararre a bangaren harkokinsa.

Ga sauran hotunan shirin bikin:

Jikar Shagari zata auri sirikin Namadi Sambo
Jikar Shagari zata auri sirikin Namadi Sambo
Jikar Shagari zata auri sirikin Namadi Sambo

Eh! Lallai Biki yayi biki!

Asali: Legit.ng

Online view pixel