Nayi mamakin yadda bikina ya kasance- Yarinyar Buhari

Nayi mamakin yadda bikina ya kasance- Yarinyar Buhari

- Yarinyar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta biyu ta bayyana gamsuwa kan yawan bakin da suka hallarci bikin aurenta

- Fatima tayi aure da burin zuciyarta, Malam Gimba Ya’u Kumo, a ranar Juma’a 28 ga watan Oktoba

Nayi mamakin yadda bikina ya kasance- Yarinyar Buhari

Yarinyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Fatima ta nuna gamsuwarta kan yadda baki da yawa suka amsa gayyatar bikin aurenta a ranar Juma’a, 28 ga watan Oktoba.

Koda dai shugaban kasa bai halarci bikin yarinyarsa ta biyu ba, amma duk da haka filin taron ya cika ya tunbatsa da manyan kasa da sarakunan gargajiya.

Fatima ta zamo matar aure ta hudu ga Gimba Ya’u Kumo, tsohon manajan-darakta na bankin Mortgage, a Daura jihar Katsina.

KU KARANTA KUMA: Hotunan Rahama Sadau tare da su Akon

Amaryan tayi Magana tare da hukumar NAN, cewa “Nayi tsananin mamaki game da yadda bikin ya kasance saboda labarin yazo ma kowa a cikin kuraren lokaci, don haka naji dadi sosai, da naga yawan mutanen da suka halarci bikin.”

Anyi auren ne bisa ga koyarwan addinin musulunci kuma ya samu halartan manyan jami’an tarayya da na jihohi.

Sun hada da gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwanbo da kuma gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abubakar.

Ministocin da suka halarci bikin sun hada da Andurrahman Dambazau (minstan cikin gida), Mansur Dan-Ali (Ministan tsaro), da kuma Kayode Fayemi (Ministan ma’adinai).

Ibrahim Idris, Inspekto-janar nay an sanda, Muhammad Babandede, shugaban masu lura da shige da fice na Najeriya (NIS); da kuma Lawal Daura, darakta-Janar na sashin jiha, sun halarci bikin.

https://youtu.be/oN38_h_cl9U

Asali: Legit.ng

Online view pixel