Muhimman labaran karshen makon da ya gabata

Muhimman labaran karshen makon da ya gabata

Jaridar Legit.ng ta tattaro muku muhimman labaran karshen makon da ya gabata

1. Allah mai iko: An haifi wani yaro da kafafu hudu

Muhimman labaran karshen makon da ya gabata

A Kasar Mozambique wani abin al’ajabi ya faru, inda aka haifi wani jinjiri da kafafu har guda hudu a jikin sa. A cewar Jaridar Magazine Independete ta Kasar, yanzu haka likitoci na kokarin aiki a kan yaron.

Likitocin Asibitin na kokarin ganin sun yi iya bakin kokarin su wajen ceto wannan yaro. Ko da yake dai har yanzu ba a bayyana jinsin jinjirin ko fito da ainihin hoton sa ba, likitoci na shirin yi masa aiki.

2. Shugaba Buhari yayi kira ga malaman addinin musulunci

Muhimman labaran karshen makon da ya gabata
President Buhari and Saudi King

Shugaba Buhari ya ja hankalin Malaman Addini musulunci na Kasar nan da cewa su rika kira kan zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kasar, Shugaban Kasar ya kira Malamai da su kuma yi kira ga zama Kasa daya tamkar ‘yan uwa. Shugaba Buhari ya kuma yi kira har wa yau da Malaman musuluncin da su koyar da mabiyan su tsoron Allah.

3. Boko Haram: An kashe wani dan kunar bakin wake

Premium Times ta rahoto cewa an harbe wani dan Boko Haram har lahira yayin da yake kokarin shiga sansani ‘Yan gudun Hijira watau IDP da ke Maiduguri. Bayan an gane sa, nan take aka shiga baza masa wuta har ya mutu.

4. Tsoron Allah ko Buhari? An maido da abincin 'yan gudun hijira da aka sace

Muhimman labaran karshen makon da ya gabata

Jami'ai a jihar Borno ta Nigeria sun ce an hannunta musu abincin da gwamnatin tarayyar kasar ta aike wa 'yan gudun hijirar rikicin Boko Haram da shi amma sai aka karkata akalar wasu daga cikin motocin da ke dauke da kayan abincin.

5. Su waye suka rike madafan iko a Najeriya [Kashi na II]?

Muhimman labaran karshen makon da ya gabata

A wancan karo mun kawo jerin wasu mutane da ake tunanin sune suka rike madafan iko a Kasar nan. A yau mun karasa kawo ragowar mutane uku kamar yadda muka yi alkawari.

6. Abba Kyari yana nan daram-dam

Muhimman labaran karshen makon da ya gabata
File photo of Alhaji Abba Kyari

Abba Kyari wanda shine shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin yace karya ce kurum ake yi, yana nan babu wanda ya kore sa, ko ya dakatar shi. Abba Kyari yace ya dai je hutu ne na kwana biyu, kuma har ya kamala, ya dawo bakin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel